KIMANIN NAIRA BILIYAN 1.4 NE HUKUMAR FANSHO JIHAR JIGAWA TA RABAWA MUTANE 564

 

Hukumar Gudanar da Tsarin Fansho na Bai-daya (Contributory Pension Scheme) ta Jihar Jigawa da suka hada da Kananan Hukumomi ta raba sama da Naira biliyan 1.4 ga ‘564.wadanda suka bar aiki
Da yake jawabi ga waɗanda suka ci gajiyar shirin a Gidan Fansho kafin rabon kuɗaɗen, Babban Akanta na Jihar Jigawa, Alhaji Abdullahi S.G. Shehu, ya bayyana tsarin fansho na Jigawa a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawu a faɗin ƙasar nan.
Babban Akantan ya jaddada ƙudurin Gwamna Malam Umar Namadi wajen kula da jin daɗin ma’aikatan gwamnati da ‘yan retiya, inda ya ce tsarin fanshon Jigawa abin koyi ne har wasu jihohi ke kai ziyara domin koyon yadda ake tafiyar da shi. Ya yaba wa gwamnan bisa jajircewarsa wajen inganta tsarin.
Alhaji Abdullahi ya ƙara da cewa tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, Gwamna Namadi ya zuba sama da Naira biliyan 11 domin ƙarfafa da inganta tsarin fansho, lamarin da ya tabbatar da kasancewarsa mafi inganci a ƙasar.
Ya bayyana cewa hukumar tana kan gaba wajen biyan dukkan haƙƙoƙin ‘yan retiya, ciki har da na ma’aikatan da suka rasu suna kan aiki.
Ya ce: “Jihar Jigawa ta fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa na Naira 70,000, wanda ya sanya albashin ma’aikatan jihar cikin mafi kyawu a Najeriya.”
A nasa jawabin, Sakataren Zartarwa na Hukumar Fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomi, Dr. Binyaminu Shitu Aminu, ya bayyana cewa adadin kuɗin da za a raba ya kai N1,429,201,208.92 ga ‘yan retiya 564, wanda ya haɗa da alawus na ritaya, alawus na mutuwa, da ragowar fanshon waɗanda suka rasu.
Dr. Aminu ya ce N1,191,804,237.17 za a biya ga ma’aikata 485 da suka yi ritaya daga aiki, yayin da N226,547,197.84 za a bai wa iyalan ma’aikata 71 da suka rasu suna kan aiki. Haka kuma, N10,849,773.91 za a raba wa iyalan ‘yan fansho 8 a matsayin ragowar fanshon mutuwa.
Sakataren Zartarwan ya sake jaddada ƙudurin hukumar na tabbatar da biyan haƙƙoƙin ‘yan fansho a kan lokaci, ciki har da biyan fansho na wata-wata tun daga ranar farko ta kowane wata.
Ya kuma nanata ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen inganta jin daɗin ma’aikatanta, domin tabbatar da cewa suna rayuwa cikin kwanciyar hankali da walwala bayan sun kammala hidimar su ga gwamnati.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version