Gwamnatin Jihar Jigawa ta kashe jimillar Naira biliyan 8.1 wajen tallafin karatu a shekarar kasafin kuɗi ta 2025, inda ta tallafa wa kusan ɗalibai 35,000 a jami’o’i da cibiyoyin ilimi na cikin gida da na ƙasashen waje, a wani ɓangare na jajircewarta wajen bunƙasa ilimi da haɓaka jarin ɗan Adam.
Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da Babban Shirin Danmodi Students Care na 2026, wanda aka gudanar a ƙarƙashin manufofin gwamnatinsa na ci gaban ɗan Adam mai haɗa kowa da kowa.
A jawabinsa, gwamnan ya bayyana shirin Danmodi Students Care a matsayin ɗaya daga cikin muhimman tsare-tsaren gwamnatinsa masu tasiri, yana mai cewa shirin ya zama wata babbar kafa ta sauyi da ke tallafa wa ɗalibai daga kowane mataki na ilimi, ciki har da almajirai a makarantun allo na gargajiya.
“Na yi matuƙar farin ciki cewa shirin ya ba da fifiko ga haɗin kai, mutunci da daraja, tare da dawo da bege da tabbatar da kyakkyawar makoma ga matasanmu. Mafi muhimmanci, shirin ya nuna jajircewar gwamnatimu wajen tabbatar da walwalar ɗalibai domin babu wani yaro da za a bari a baya,” in ji gwamnan.
Gwamna Namadi ya jaddada cewa zuba jari a kan al’umma, musamman ta fuskar ilimi, na daga cikin ginshiƙan Manufofinsa guda 12 na “Greater Jigawa”, yana mai cewa matasan jihar su ne alfahari, ƙarfi da kuma makomar cigaban ta na dogon lokaci.
Ya ƙara da cewa manufofin gwamnatinsa an tsara su ne domin tabbatar da adalci, mutunci da dama iri ɗaya ga kowa, musamman mata, masu larura da kuma yaran da ba sa makaranta.
Dangane da girman tallafin, gwamnan ya bayyana cewa cikin Naira biliyan 8.1 da aka kashe a 2025, akwai ɗalibai sama da 230 daga Jigawa da ke karatu a manyan jami’o’i na ƙasashen waje, musamman a fannonin likitanci da injiniya, baya ga dubban ɗalibai da ke karatu a manyan makarantu a cikin Najeriya.
A ɓangare na Shirin Danmodi Students Care na 2026, gwamnan ya sanar da wasu tsare-tsare na ƙarfafa ɗalibai da suka haɗa da:
Rarraba kayan karatu da kayan makaranta ga yara 25,000 da ba sa makaranta;
Samar da kekuna 300 da keken guragu domin sauƙaƙa zirga-zirga ga ɗaliban sakandare da yara masu nakasa;
Rarraba kwamfutoci 100 ga ɗaliban Jigawa da ke karatu a Kwalejin ’Yan Sanda ta Najeriya (Wudil) da Kwalejin Sojoji ta Najeriya (Kaduna);
Ƙarfafa almajirai 2,500 da malamai 287 na makarantun allo, domin ƙarfafa manufar ilimi mai haɗa kowa da kowa a jihar.
Gwamnan ya buƙaci waɗanda suka amfana da shirin da su yi amfani da damar da aka ba su yadda ya kamata, tare da kira ga masu ruwa da tsaki su ci gaba da haɗa kai domin ɗaga darajar ilimi a jihar, yana mai jaddada cewa babu wani yaro da za a bari a baya.
Ya kuma yaba wa Ofishin Danmodi Students Care bisa jajircewa da ƙirƙira, tare da ƙarfafa shi da ya ci gaba da aiwatar da hangen nesan gina “Greater Jigawa” ta hanyar ilimi da ci gaban ɗan Adam.
Tun da farko, Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Harkokin Ɗalibai, Muhammad Salisu Seeker, ya bayyana cewa cikin shekaru biyu da rabi kacal, shirin Danmodi Students Care ya zama sananne a faɗin jihar Jigawa, inda ya amfanar da ɗalibai sama da 250,000 kai tsaye.
Ya ce shirin ya taimaka wajen samar da guraben karatu ga ɗalibai sama da 15,000 a jami’o’i da kuma 40,000 a kwalejojin ilimi, polytechnics da monotechnics, tare da rage yawan barin makaranta ta hanyar rarraba kayan makaranta 55,000, jakunkunan makaranta 55,000 da littattafan rubutu 200,000.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version