KOTUN KOLI TA YI WATSI DA SHARI’AR ZARGIN KISAN KUDIRAT ABIOLA DA AKA TUHUMI HAMZA AL-MUSTAPHA
Kotun Koli ta Nijeriya ta yi watsi da shari’ar da ake yi wa tsohon babban jami’in tsaron marigayi shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha, wato Major Hamza Al-Mustapha, dangane da kisan marigayiya Kudirat Abiola.
Kudirat Abiola ita ce matar marigayi attajiri kuma ɗan siyasa, Cif MKO Abiola, wanda ake ganin shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni, 1993, wanda tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Babangida ya soke.
An kashe Kudirat Abiola ne a jihar Legas a lokacin rikice-rikicen da suka biyo bayan soke zaɓen, yayin da take ci gaba da fafutukar ganin an maido da sakamakon zaɓen da gwamnatin soja ta soke.
Shari’ar da gwamnatin jihar Legas ta shigar kan Al-Mustapha kan zargin kisan ta, ta zo ƙarshe ne bayan hukuncin da kwamitin alkalan Kotun Koli su biyar, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Uwani Aba-Aji, suka yanke.
Kotun Koli, a hukuncin da ta yanke baki ɗaya, ta ce gwamnatin jihar Legas ta nuna kamar ta daina sha’awar shari’ar, don haka aka ɗauka ta yi watsi da ita.
Mai shari’a Aba-Aji ta bayyana cewa shekaru tara sun isa a ce mai ƙara ya shigar da sanarwar ƙorafi da kuma takardar ƙorafi a gaban kotu, amma hakan bai faru ba.
Haka kuma, Kotun Koli ta nuna ɓacin rai kan yadda babu wani lauya da ya wakilci gwamnatin jihar Legas, tare da rashin bayar da wani bayani ga kotu da kuma wanda ake ƙara, duk da cewa an aika da sanarwar zaman kotu tun daga shekarar 2020.
Saboda haka, kotun ta yanke hukuncin watsi da shari’ar gaba ɗaya.
