Kungiyar musulmi kwararru ta fanni daban – daban da ke Yada addinin Musulunci ta ziyarci wani yanki dake karamar hukumar Rogo, yayin da ta baiwa Mata masu zaman kansu magunguna da kuma tallafi na Jari domin Dogaro da kai.

Shugaban kungiyar Alh Adamu saleh kwaru shine ke jagorantar gudanar da harkokin kungiyar, tare da hadin gwiwar, kungiyar likitocin Asibitin Malam Aminu kano,IMAN,.

 

 

Yayin da kuma aka gudanar da wa, azi ga kristocin yankin domin su shigo Addinin musulinci, da mata masu zaman kansu tare da yin kira su koma ga gidajen iyayen su ko mazajensu, domin samun kulawa da kuma kaucewa sabon Allah madaukakin sarki.

Shugaban kungiyar Alh Saleh Adamu Kwari ya bayyana cewar AL, ummar karamar hukumar Rogo sun Amfana da magunguna da aka dubasu aka basu na tafi da gidan ka.

Mai baiwa kungiyar shawara Akan harkokin SHARI, a Barr, Yahaya Ibrahim Aliyu, ya Ja hankalin mawadata da su taimakawa wannan kungiyar dake Yada Addinin musulinci da bada magunguna kyauta ga marasa lafiya.

 

Screenshot 20260430 074230

Mutane fiye da 700 ne suka Amfana da wannan tallafin na bada magani kyauta. Tare da gudanar da wa, azi ga maguzawa da kristoci. da fito da Daurarru.

Dr imam mal Rabiu wadda shine secretary kuma yawakilci shugaban Kungiyar Iman daga asibin mal Aminu kano wato Dr Gaya, dayawansu anyimusu gwaje gwaje wasu anbasu magani wasu kuma birni za’a kawosu ayimusu aiki dafatan Allah yasakawa duk wanda yasaka share dinsa awannan gagarumin aiki,

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version