Makon da yagabata ne dai gwamna Jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf ya tsunduma acikin jam, iyyar Apc bayan da yayi fatali da jam, iyyar NNPP sakamakon cukumurdar da taki ci taki cinyewa.

Wannan tasa arana tsaka aka ga Tsohon shugaban jam, iyyar Apc na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje da DSP, da shugaban jam, iyyar Apc na Jihar kano Alh Abdullahi Abbas, sanata Barau I Jibrin da sanata kawu sumaila da shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan kasar hausa Mai tuta a gidan Gwamnatin Jihar kano. suna musabaha da Gwamnan Jihar Kano, da sauran kusoshin gwamnati,harma dai a karshen zance ma dai suka daga Hannun gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin shine Alkiblar Jihar kano a Karo na biyu zaben shekara ta 2027.

 

Wannan abin Alfarahari ne  domin kuwa an samu hadin Kai tsakanin shugabannin AL, umma Akan manufa guda ta ciyar da Jihar kano gaba ta fuskar tattalin Arzikin kasa da zaman takewa.

Hakance tasa da hadin gwiwar shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa da shugaban karamar hukumar Doguwa Alh Abdurrashid Rilwan da Hon Umar Haruna Doguwa kwamishinan ruwa na Jihar kano Eng Ado Ibrahim Doguwa da Hon mamuda Hudu Doguwa tsohon shugaban karamar hukumar Doguwa sauran jiga – Jigan Yan siyasa na yankin karamar hukumar Doguwa sun hade waje guda abinda Ana iya cewa wannan shine Karon da aka samu wannan hadin Kai tun Bayan da aka yiwa jam, iyyar PDP bara, a.

Wannan tafiya Bata bar kowa ba a karamar hukumar har da sanata ma, Ud El-jibril Doguwa da Mai neman kujerar shugabancin karamar hukumar Doguwa Hon Shu, aibu Rabilu Doguwa, duk an dinke waje guda ma, ana dai APC ta dauki saiti layin guda daya ne Dodar.

 

An gudanar bikin karbar Katin shaidar jam, iyyar Apc na Jihar kano, yayin da Hon Umar Haruna Doguwa kwamishinan ruwa da eng Ado Ibrahim Doguwa da Hon Abdurrashid Rilwan da shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Doguwa Alh sule Abdu Mai Mai ya basu kan aka Hannu waje guda, aka daga dake nuna alamar tsintsiya madaurinki daya.

. Anyi jawabai da Bayanin nuna hadinkai tun acikin garin Doguwa daga nan akaje Babban Dakin taro na multipurpose Hall dake Sabon garin Dadin kowa, anan ne ma mukanji Hon Umar Haruna Doguwa yana cewar dama sune, yanzu Kuma kowaye yazo mana da wasa ko shakiyanci irin na siyasa mune zamuyi maganinsa, yadda Gwamnan Kano yake son cigaban Jihar kano, haka mukeson cigaban yankin kananan hukumomin tudun wada da DOGUWA, saboda haka nema Doguwa da Tudun wada Sai Rt Hon Alhassan Ado Doguwa.

Fatan wannan hadin kai zai zama abin misali da kwatance ta fuskar cigaba.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version