Gwamnatin Jihar Kano (KNSG) ta sake jaddada ƙudurinta na bunƙasa aikin jarida na zamani (digital journalism) bisa ƙa’idojin ɗabi’a, nagarta da ƙwarewa, inda ta bayyana kafafen yaɗa labarai a matsayin muhimmin ginshiƙi na tafiyar da mulkin dimokiraɗiyya.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake buɗe taron bitar kwanaki biyu ga mambobin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Intanet ta Kano (Kano Online Media Chapel) ƙarƙashin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), wanda aka gudanar a Dutse, Jihar Jigawa.
Kamar yadda ya bayyana, ya zama wajibi ‘yan jarida su guji yaɗa labaran da ke cike da tayar da hankali, son yin gaggawar wallafa labarai ba tare da cikakken bincike ba, da kuma labaran da ba su da inganci.
Kwamishinan ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da yake bai wa ɓangaren aikin jarida da kuma kare ‘yancin faɗar albarkacin baki. Ya ƙara da cewa aikin jaridar zamani (digital journalism) ya zama muhimmin ginshiƙi a aikin jarida a ƙasar nan, kuma ya cancanci cikakkiyar kulawa da girmamawa.
Ya ja hankalin ‘yan jarida kan muhimmancin gina suna (brand) ta hanyar gaskiya, riƙon amana, jajircewa da ɗorewa, yana mai cewa nasarar wasu a kafafen yanar gizo ba ta zo ne bisa sa’a ba, illa sakamakon ƙwazo da sadaukarwa.
A nasa jawabin, Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ga Gwamnan Kano, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda Mustapha Muhammad, Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna ya wakilta, ya buƙaci ‘yan jarida su rungumi sabon salo na aikin jarida da ke fifita ɗa’a da anfani ga al’umma fiye da riba ta kuɗi.
Ya ce ‘yan jarida na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunanin al’umma ta fuskar zamantakewa, siyasa da tattalin arziƙi, yana mai cewa aikin jarida ya kamata ya zama hidima ga jama’a.
Shugaban NUJ na Jihar Kano, Kwamared Sulaiman Dederi, ya yaba wa Kwamishinan Yaɗa Labarai bisa hangen nesa da jajircewarsa wajen shirya taron. Ya ce taron ya zo a daidai lokacin da aikin jarida ke fuskantar sauye-sauye sakamakon fasahar zamani da ƙalubalen ɗa’a.
Haka nan, Shugaban NUJ na Jihar Jigawa, Kwamared Ismaila Ibrahim, ya ce a wannan zamani da bayanai ke yawo cikin sauƙi, nauyin da ke kan ‘yan jarida ya ƙaru sosai, kasancewarsu masu tsaron gaskiya da muradin al’umma. Ya kuma sanar da shirin buɗe Online Chapel a Jihar Jigawa nan ba da jimawa ba, tare da inganta cibiyar ICT da dawo da intanet kyauta ga ‘yan jarida.
Tun da farko, Shugaban Kano Online Journalists, Kwamared Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya ce ƙungiyar ta kuduri aniyar ci gaba da gina ƙwarewar mambobinta, tare da yaba wa Gwamnatin Jihar Kano da Kwamishinan Yaɗa Labarai bisa ɗaukar nauyin taron.

