Sarkin Sudan Gaya, Alh Musa Ahmad Abba, ya karrama Hajiya Hafsat Ahmad Abba da Sarautar Giwar Sarkin Sudan.
Giwar sarki sarauta ce da ake karrama iyaye Yan, uwa da iyalai da ita musanman ma Mata, sakamakon irin karamci da mukami da kusanci da mutum yake dashi ga Mai sarautar..
A cikin takardar nadin da ya bayar da hannun sa Mai martaba Sarkin Sudan Gaya Dr, musa Abba Ahmad muna cikin farin ciki sa ga Godiya ga Allah madaukakin sarki bisa bashi Ikon gabatar da takardar Amincewa ga babbar Yaya agaremu, Basarakiya,Sayyada, Hafsat Ahmad Abba,,abin alfahari cikin masarautarmu—inda muke naɗa ta tare da girmamawa ta musamman babbar yayar Sarki, mace mai daraja da mutunci, zuwa sarautar Giwar Sarkin Sudan
Wannan ba nadi kawai ba ne, nadi ne mai cike da girmamawa da ɗaukaka, da karamci, domin an ɗora wa wadda ta cancanta bisa halaye da ɗabi’u na gari, da Addini da AL, ada irin ta hausa fulani wadda ta riga ta zama abin koyi a cikin al’umma,
ginshiƙin ladabi da kamun Kai da kawaiici a tarbiyya,
tushen zaman lafiya da haɗin kai,mai tausayi da hakuri.
Wannan abin alfahari ne ga gidan sarauta baki ɗaya.
A matsayinta na babbar yaya ga Sarki, wannan matsayi ya ƙara mata wata daraja,da girma ta musamman wadda ke ƙara haskaka martabar masarauta da kuma ƙarfafa haɗin kan gidan sarauta.
Mun naɗa ta ne da girmamawa, da amincewa, da kuma cikakken yabo, bisa cancanta da kuma amana da muke da ita gare ta.
Allah Ya ƙara mata ɗaukaka, Ya sa wannan sarauta ta zama tushen alheri, zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Wannan shine Bayanin Mai martaba Sarkin Sudan Dr, Alh Musa Ahmad Abba.
Anata bangaren Giwar sarkin Sudan Hajiya Hafsat Ahmad Abba ta yi fafinciki bisa wannan sarautar da Dan, uwa Mai martaba Sarkin Sudan Dr, Musa Ahmad Abba ya yi Mata kana tayi godiya Gareshi bisa nuna kauna da karamci da yayi Mata.
Yan, uwa da Abokan Arziki da dama ne suka yi farin ciki ga wannan nadin da akayi.
