ZAMU DUBA ABINDA YAKAMATA MUYIWA RT HON ALHASSAN ADO DOGUWA, INJI SARKIN LERE ENG SULEMAN UMAR.

Cikin yanayi na wasan zage – zage da kanawa Mai martaba Sarkin Lere yake bayyana cewar Rt Hon Alhassan Ado Doguwa, Kasancewar sa ba kano mukuma zage, kasan ba kano Sai a sashin a Hanya.
Mai martaba Sarkin Lere ya Yabawa Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan kasar hausa Mai tuta bisa yadda yake kokari wajen sada zumunci tsakanin sa da AL, ummar yankin na Lere dake Jihar Kaduna.
Sarkin na wannan yabonne a wajen Bikin kaddamar da kalandar kungiyar cigaban Lere Lere Development Association ta kaddamar a Garin lere dake Jihar Kaduna.

Muna Godiya ga Hon Alhassan Ado Doguwa Muna tura masa gayyata Akant Abun Alheri na cigaban kasa na karamar hukumar Lere yana kuma yin kokari yazo ko ya turo wakilci, Muna Godiya da kauna da zumunci da ake nuna mana.

Munji dadi kwarai dangane da wannan.

Mai martaba Sarkin Lere ya Kara da cewar kungiyar Lere Development Association kungiyace da matasa suka dauki gabarar taimakawa Dalibai da Samarda Hasken Wutar Lantarki, da gyaran ofishin Yan Sanda.

Muna Godiya ga Rt Hon Abbas TAJJUDEEN Iyan zazzau bisa wannan tagomashin na baiwa Matasan mu aiki, da kuma Rt Hon Alhassan Ado Doguwa da yake zuwan mana da Abubuwan Alheri.

Muna Godiya ga Rt Hon Alhassan Ado Doguwa kusan Dan mu ne Dan Lere ne abinda ya rage mana kawai shine mu shine mutabbatar masa da shi Dan Lere ne, mu tabbatar masa da wani Babban Abu Wanda masarautar Lere zatayi masa Wanda duk inda yaje yayi Shima ya nuna Dan Lere. ne

Munji Ana ta fada masa sardaunan Rano, sardaunan kasar hausa Mai tuta to mu Abinda zamuyi masa IN SHA ALLAH zai zama wani Abu da zaiyi Alfahari dashi.

Majalisar masarautar Lere tana nan tana nazari IN SHA ALLAH Bada daɗewa ba zata sanar da Hon Alhassan Ado Doguwa na lokacin da ya kamata karrama shi, a tabbatar masa dashi shi ba suruki bane kawai shi Da, ne kuma ya cancanci a yaba masa.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version