An bukaci mataimakin Gwamnan Jihar kano da ya Yi Murabus Nan Take
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya bukaci Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Gwarzo, da ya yi murabus daga mukaminsa.
Waiya ya yi wannan kira ne bayan da Mataimakin Gwamnan ya ƙi bin sahun Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen sauya sheƙa daga NNPP, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A cewar Kwamishinan, matsayar da Mataimakin Gwamnan ya dauka ba ta dace da tsarin tafiyar da gwamnati ba, tare da jaddada cewa murabus zai zama mafita mafi dacewa a irin wannan hali.da ake ciki na siyasar wannan zamani wannan na nuni da cewar, Akwai yiyuwar a tsige shi Muddin dai yaki bi ta ruwan sanyi

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version