A yanzu haka dai ana iya cewa Inna ta San kalwa kalwa tasan Inna domin kuwa, sakamakon musayar wuta irin ta siyasa da aka yi tsakanin Yan gwagwarmaya magoya bayan DSP Sanata Barau I Jibrin maliya da Yan gwagwarmaya na Gidan Hon AA Zaura, Babban mataimaki Akan kafafen Yada Labarai ga DSP Sanata Barau I Jibrin, wato kwamared Adamu Abdullahi karkasara, ya yi kira ga y’an gwagwarmaya na Gidan Sanata Barau I Jibrin da su Ajiye makaman su na yakin siyasa Akan AA Zaura azo ayi tallan APC.

Wannan ya biyo bayan wata sanarwa da karkasara ya fitar yana mai cewar, dama Yan gwagwarmaya da sanata Barau I Jibrin ba masu neman rigimar siyasa bane basa gaba da kowa, azo ayi jam, iyyar Apc domin kaiwa ga gaci.

Haka zalik Kwamared Adamu Abdullahi karkasara ya Mika godiya da jinjina ga dukkan Yan gwagwarmaya na Gidan DSP bisa yadda suka fito a kafafen Yada Labarai suka kare Kima da martabar Sanata Barau I Jibrin.

Adamu karkasara ya bayyana cewar zasu cigaba da hadakai da dukkan Wanda yazo ya bada gudunmawar cigaban Apc da manufofin Sanata Barau I Jibrin dan Kai shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ga gaci a zaben shekara ta 2027

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version