Akasar hausa Kamar yadda magabata sukayi musanman a bangaren sarauta Akan nada mukamai da dama ciki harda sarauta da ake baiwa Mata, musamman ma mahaifiya.
Mai Babban daki sarautace ta karramawa da mutuntawa da girmamawa, wadda ake bada ita ga Mai fada aji musanman uwa maba da mama ko makamanciyar haka.

Mai martaba Sarkin Sudan Gaya Sarkin Sudan, Alh Dr Musa Ahmed, ya bawa Mahaifiyarsa mai daraja, madogarar albarka, ginshikin rayuwa, Hajiya Amina Ahmad, sarauta ta girma, Mai Babban Daki. Wanna sarauta ce ta girmamawa da daraja da daukaka.
Wannan na nuni da cewar laya tayi kyan rufi bisa LA, akari da yadda aka gudanar da wannan Babbar kyauta ta sarauta kuma aka sadakar da it ga mahifiya
Muna rokon Allah Ya karawa Mai Babban Daki lafiya da tsawon rai, cikin imani.