Sanata Abdulkarim Abdussalam da aka fi Sani da suna AA ZAURA ya bayyana Iftila’in gobara da ya Afku a sashin kasuwar singa dake Jihar kano da cewar Babban lamari ne da ya tayar da dukkanin hankalin Mai tunani, musanmam ma idan akayi la akari da halin da ake ciki na tattalin arziki da masu karamin karfi da ke neman na Abinci a kasuwar.
Kasancewar kasuwar singa Babbar kasuwa ta yankin Afrika ta yamma da ke gudanar harsaye da sayarwa

Wata sanarwa da Mai magana da yawun Sanata AA Zaura ya baiwa jaridar muryar Arewa Ayau, Hon Dahiru Ahmad Mai huddadu, yace Sanata Abdulkarim Abdussalam AA Zaura ya bukaci da asamo hanyoyin da za, a magance matsalolin da ke addabar kasuwar ta singa da suka hada da samar da hanyoyin kashe gobara da za, a iya shawo kanta batare da ta yi ta, adi da yawaba.
Hon Mai huddadu Sanata Zaura yayi Kira ga masu hannu da shuni da su kaiwa wadanda Iftila’in gobarar ya shafa da tallafi domin sunyi Asarar miliyoyin kudi da kayan Abinci kana Akwai bukatar a tallafa Dan su cigaba da gudanar da Harkokin su na yau da kullum, na neman Abinci
Sanata Abdulkarim Abdussalam AA ZAURA yayi Addu, ar Allah ya kiyaye Faruwar hakan a gaba, yayi Addu, ar Allah ya mayar musu da Alheri