Excellency AA ZAURA Yasha Alwashin cigaba da baiwa Jami, an tsaro tallafin da ya dace domin karfafa musu gwiwa.

An bukaci AL, umma da su cigaba da baiwa Jami, an tsaro hadin Kai da goyan baya domin Inganta tsaro, acikin sako da lungun na Jihar kano.

Tsohon Mai neman kujerar Sanatan Kano ta tsakiya, Sanata AA Zaura shine yayi wannan kiran ta bakin Mai magana da yawun sa Hon Dahiru Ahmad Mai huddadu shine yayi wannan kiran a ofishin Yan Sanda na Sharada dake Ja, en karamar hukumar Gwale dake Jihar kano.

Hon Dahiru Ahmad Mai huddadu yace Al, umma suna da rawar da zasu taka wajen tallafawa Jami, an tsaro da mahimman bayanai da suka dace dan Inganta tsaro da kuma Kai rahoton dukkanin wani abu da basu aminta dashi ba.
Sanata AA Zaura yabada kudi kimanin naira dubu Dari biyu amatsayin tallafi.

Anasa jawabin kwamishinan Yan sanda Jihar kano, Wanda Baturen Yan sandan sharada Ja, en Abdurrashid ya wakilta ya bayyana ya Yabawa Sanata AA ZAURA bisa yadda yake baiwa Rundunar Yan’sandan Jihar kano hadin Kai da goyan baya da cigaban aikin su.

Babban Baturen Yan sandan dake sharada ya bayyana cewar sun baiwa Jami, an sintiri masu yawa horo domin suyi kafada da kafada da dukkan wani kalubalen tsaro da ka iya Kai komo a yankin na karamar hukumar gwale da kewaye,domin samun kwanciyar hankali da zaman lafiyar AL, umma.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version