Wata sanarwa da ta fito daga Gidan Radion nasara ta bayyana cewar, Fitaccen masani a fannin ilimi da yada labarai, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya yi ritaya daga Jami’a.
Ya cika shekaru 70 da haihuwa a ranar Asabar 25 ga Afrilu 2026.
Cikin wata sanarwa, Farfesa Adamu ya godewa Allah SWT bisa wannan dama ya bashi wajen gina rayuwa a fannin ilimi da bincike kusan shekaru 48 a jami’a.
Farfesa Adamu ya fara aiki a Jami’ar Bayero ta Kano a shekarar 1980 kuma ya zama Farfesa a Tsangayar Ilimi da kuma Tsangayar Sadarwa.
Ya taba rike mukamin Shugaban Jami’ar Karatu Daga Gida ta Najeriya wato NOUN..
Tun a shekarun baya Farfesa Abdallah ya zamanto Babban Malami da yayi ruwa yayi tsaki wajen ceto harkar wasan kwaikwayo a Arewacin Nijeriya, Amma sakamakon wasu dalilai wasu suka kawo wa harkar tarnaki da shakulatin bangaro, har ma dai harkar film din ta zama yadda take a halin yanzu.
Masana da masu hasashe da hangen nesa sunyi hasashen cewar da masu masana, antar harkar wasan kwaikwayo ko harkar film sun bi tsarin shehin malamin da yanzu ta wuce sanin Yaro.
