GWAMNA UMAR NAMADI YA KADDAMAR DA SABUWAR JAMI’AR KIMIYYA DA SAMAR DA LIKITOCI DA BADA HORO GA JAMI, AN KIWON LAFIYA DOMIN INGANTA HARKAR LAFIYA

Gwamnatin Jihar Jigawa ta karɓi mallakar Jami’ar Khadija da ke Majia a hukumance, bayan sayen ta daga hannun mai zaman kansa, tare da sauya mata suna zuwa Jami’ar Jihar Jigawa ta Kimiyyar Likitanci da Lafiya (JSUMAHS), Majia.
An gudanar da bikin a ranar Talata a garin Majia, inda Gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranci taron tare da wasu mambobin Majalisar Zartarwa ta Jiha, ‘yan Majalisar Dokoki ta Jiha, sarakunan gargajiya da sauran manyan masu ruwa da tsaki.
Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Namadi ya bayyana wannan mataki a matsayin wani muhimmin cigaba a bangaren ilimi a jihar.
“Yau wata muhimmiyar rana ce a kokarin da muke yi na inganta ilimi a Jigawa. Muna kammala wani tsari da muka fara shekaru biyu da suka gabata na karɓar Jami’ar Khadija daga hannun masu zaman kansu,” in ji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa dalilin sayen jami’ar shi ne domin faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimin likitanci tare da samar wa matasa ƙarin dama.
“Mun yanke shawarar sayen wannan jami’a ne domin ƙara wa matasanmu damar samun ilimi mai inganci.”
Ya kuma ƙara da cewa tuni gwamnati ta fara gyaran gine-gine da kuma kafa ingantaccen tsarin gudanarwa domin tabbatar da jami’ar ta zama cikin manyan jami’o’i a ƙasar nan.
“Mun fara inganta ababen more rayuwa, kuma muna yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da jami’ar ta zama daga cikin mafi inganci a Najeriya.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa wannan mataki zai rage yawan daliban da ake turawa ƙasashen waje domin karatun likitanci.
“A halin yanzu muna da dalibai sama da 180 da ke karatun likitanci a ƙasashen waje. Wannan jami’a za ta taimaka wajen rage kashe kuɗaɗen ƙasashen waje ba ga Jigawa kaɗai ba, har ma da Najeriya baki ɗaya.”
Haka kuma, ya yabawa wanda ya kafa jami’ar, Dakta Musa Adamu Majia, bisa gudunmawar da ya bayar.
“Tarihin ilimi a Jigawa ba zai cika ba tare da ambaton sunanka ba,” in ji gwamnan.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa jami’ar cikakken goyon baya.
“Muna tabbatar muku da cewa gwamnati za ta ci gaba da mara muku baya domin nasarar wannan jami’a.”
A nasa bangaren, Mataimakin Shugaban Jami’a (Vice Chancellor), Farfesa Mahmoud U. Sani, ya bayyana wannan sauyi a matsayin mataki mai muhimmanci kuma na hikima.
“Wannan mataki ba kawai na gudanarwa ba ne, illa wata babbar dabara ce ta shugabanci mai hangen nesa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wannan jami’a za ta taimaka wajen magance ƙarancin ma’aikatan lafiya a jihar da yankin Arewa baki ɗaya.
“Wannan jami’a ita ce ta farko mallakin jiha a Arewacin Najeriya da ta kware a fannin kimiyyar likitanci da lafiya, wanda ke sanya Jigawa a sahun gaba a wannan fanni.”
Shi ma Shugaban Kwamitin Sauyin Mallaka, Dakta Lawan Yunusa Danzomo, ya bayyana cewa an gudanar da dukkan matakan karɓar jami’ar cikin gaskiya da bin ƙa’ida.
“Wannan biki na nuna kammala wani tsari mai tsafta, gaskiya da haɗin gwiwa domin amfanin jama’a.”
Ya ƙara da cewa yanzu jami’ar ta shiga sabon babi na cigaba.
“Kammala wannan tsari na nufin fara wani sabon mataki na bunƙasa wannan jami’a.”

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version