Ƴan majalisar wakilai huɗu daga Kano sun sauya sheka daga NNPP zuwa ADC
Ƴan majalisar wakilai guda hudu daga jihar Kano sun fice daga jam’iyyar NNPP zuwa ADC.
Ƴan majalisar sun hada da Sani Wakili mai wakiltar Minjibir/Ungogo, Muktar Zakari daga Tarauni, Umar Datti mai wakiltar Kura/Madobi/Garun Mallam, da kuma Abdulhakeem Ado daga Wudil/Garko.
Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ne ya karanta takardun sauya shekar ta su a zaman majalisar na yau Laraba.
