Zababben Gwamnan Jihar kano Abba Gida Gida ya mika sunan Murtala Sule Garo ga majalisar dokokin Kano don tantancewa a matsayin mataimakin Gwamna

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aike da sunan Alhaji Murtala Sule Garo ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da amincewa da shi a matsayin mataimakin gwamna.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar.

Sanarwar ta ce matakin ya yi daidai da sashe na 191(3) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda ke bai wa gwamna damar nada mataimaki idan mukamin ya zama babu kowa.

Ta kuma tunatar da cewa kujerar mataimakin gwamna ta zama babu kowa ne bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna, Abdussalam Gwarzo, a ranar 27 ga Maris, 2026.

Gwamnan ya bayyana cewa nadin ya biyo bayan tuntuba da masu ruwa da tsaki, inda ya bukaci majalisar dokokin jihar ta amince da nadin.

Alhaji Garo mai shekaru 48, gogaggen dan siyasa ne da ya shafe sama da shekaru 20 yana rike mukamai na zabe da na nadin gwamnati. Ya taba zama Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyarsa a jihar, mai ba gwamna shawara, da kuma shugaban karamar hukumar Kabo.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version