Anja hankalin Yan kasuwa da malamai da Yan boko da mawadata dasu tallafawa mabukata, domin samun kyakykyawan rabo a ranar Alkiyama.

Sanata Abdulkarim Abdussalam AA ZAURA shine yayi wannan kiran ta bakin Mai magana da yawun sa Hon Dahiru Ahmad Mai huddadu,

Mai Huddadu na wannan batunne Alokacinda ya Ke jajantawa Yan kasuwar singa da Iftila’in gobara Yaa sake afkawa a Karo na biyu.

Hon Dahiru Ahmad Mai Huddadu yace Sanata AA ZAURA ya Samarda motocin kashe gobara da zasu tallafawa AL, ummar Jihar kano da kewaye.

AA ZAURA ya jajantawa Yan kasuwar da kuma yin kira da su kasance masu bada sadaqa da kyauta tawa na kasa domin maganin masifu Kamar yadda Annabin Tsira yayi umarni acikin hadisin sa.

Sanata AA ZAURA YA bukaci a tallafawa mabukata acikin wannan wata Mai Albarka

AA ZAURA yayi fatan Allah ya kiyaye faruwar hakan a gaba

 

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version