Dan majalisar wakilai na tarayya eng Sani Bala tsanyawa ya shawarci wadanda Allah ya horewa da su taimakawa na kasa dasu, musanman acikin wannan wata Mai Albarka watan Ramadan.
Hon Sani Bala tsanyawa na yin wannan batunne Alokacinda yake jajantawa Yan kasuwar singa bisa Iftila’in gobara da ya afka musu.
Tsanyawa yace Akwai bukatar a sauya wasu tsare – tsare da ke kawo cikasa a yanayin kasuwanci na Samarda kyakykyawan yanayi na saye da sayarwa a kasuwar ta singa.
Eng Sani Bala tsanyawa yayi Addu, ar Allah ya kiyaye afkuwar hakan nan gaba tare da fatan Allah ya mayar da Abinda suka rasa
Hon Sani Bala tsanyawa ya Taya Al, ummar musulmi da Gwamnan Jihar Kano eng Abba Kabir Yusuf da AL, ummar yankin Ghari da Tsanyawa dama Jihar kano murnar fara Azumin watan Ramadan da fatan Allah ya karbi ibadunmu Allah ya sa Agama lafiya
