Hukumar Zaben Najeriya INEC ta ayyana Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord Party a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar jiya Asabar.

Adeleke ya samu wa’adi na biyu bayan ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC.

Jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan Osun, Joshua Ogunwole, ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zabe ta Hukumar Zaben Najeriya (INEC) da ke Osogbo da safiyar Lahadi.

A cewarsa, Adeleke ya samu kuri’u 511,067, wanda ya ba shi nasarar lashe zaben.

Dan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya zo na biyu da kuri’u 444,815, yayin da Najeem Salaam na jam’iyyar ADC ya zo na uku da kuri’u 17,180.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version