APC Ta samu karuwa Jigawa Yayin da Gwamna Namadi Ya Karbi mutane i 4,000 a yankin Taura
Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Jigawa na ci gaba da samun karbuwa yayin da Gwamna Malam Umar Namadi ya karbi kimanin sabbin mambobi 4,000 da suka sauya sheka daga jam’iyyun adawa daban-daban.
An gudanar da wannan gagarumin taro ne a ranar Talata a karamar hukumar Taura, inda aka kuma kaddamar da sabon sakatariyar jam’iyyar APC a yankin, lamarin da ke kara nuna karfin jam’iyyar a matakin kasa da kasa.
Sabbin mambobin, karkashin jagorancin tsohon dan siyasa kuma tsohon shugaban jam’iyya a jiha, Hon. Safiyanu Ubale Taura, wanda ya taba zama dan majalisar wakilai har sau hudu a karkashin jam’iyyar PDP, an bayyana su a matsayin masu tasiri sosai a siyasar kananan hukumomin Taura da Ringim.
Da yake jawabi ga dimbin jama’a da suka halarci taron, Gwamna Namadi ya bayyana cewa sauya shekar na nuna yadda jam’iyyar APC ke kara samun karbuwa a fadin jihar Jigawa. Ya ce mutanen da suka sauya shekar sun kasance ginshikin adawar siyasa a baya, amma yanzu sun rungumi jam’iyya mai mulki.
“Wannan al’amari ya nuna cewa APC ita ce jam’iyyar da al’ummar Jigawa suka fi so. Mutanen da muka karba a yau su ne ginshikin hada kan jama’a a Taura da Ringim,” in ji gwamnan.
Ya kuma jaddada cewa yawan sabbin mambobin da jam’iyyar ke samu ya fi duk wata asara da aka samu na masu fita daga cikinta, yana mai cewa APC na kara karfi a dukkan kananan hukumomin jihar.
Gwamna Namadi ya yi wa sabbin mambobin alkawarin adalci da hadin kai tare da shugabanci mai gaskiya da rikon amana.
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Hon. Ahmed Garba M.K., ya ce jam’iyyar na fuskantar yawaitar sauya sheka a baya-bayan nan, wanda ya danganta da salon shugabancin Gwamna Namadi da kuma ayyukan ci gaba da gwamnatin ke aiwatarwa.
Ya kuma misalta aikin samar da wutar lantarki a Taura, wanda ya dawo da haske bayan fiye da shekaru goma na duhu a garin da kewaye, a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka jawo goyon bayan jama’a ga APC.
Shi ma da yake jawabi, Hon. Safiyanu Ubale Taura ya tabbatar da cikakken goyon bayan sa da na mabiyansa ga jam’iyyar APC da gwamnatin Namadi, yana mai alkawarin yin aiki tukuru domin ganin nasarar jam’iyyar a zabuka masu zuwa.
“Mun kuduri aniyar tabbatar da nasarar wannan gwamnati, kuma za mu hada kan magoya bayanmu domin ci gaba da wannan tafiya. Haka kuma za mu ba da shawarwari domin inganta rayuwar al’umma,” in ji shi.
Taron ya samu halartar dubban magoya bayan jam’iyya da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na karamar hukumar Taura da ma wajenta, abin da ke kara tabbatar da karfin APC a jihar Jigawa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version