Wata motar tirelar dakon kaya ta ƙone kurmus a garin Karfi da ke Karamar Hukumar Kura a Jihar Kano, a safiyar ranar Asabar 10 ga Janairun 2026.

Arewa Updates ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne bayan da direban motar ya kammala shan mai, yana kokarin hawa babban titi, a nan ne tirelar ta tuntsura ta fada cikin rami.

Bayan shafe wasu sa’o’i da faduwar motar, sai ta kama da wuta, lamarin da ya janyo konewar motar gaba daya tare da kayan da ta dauko.

Jami’an kashe gobara na Jihar Kano tare da taimakon motar kashe gobara ta gidan man Salbas sun garzaya wurin, inda suka kashe wutar.

Rahotonnin da muka samu sun nuna ba a samu asarar rai ko rauni ba, domin direban motar da wakilin mai kaya tare da yaran motar duk sun tsira a lokacin da lamarin ya faru.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version