Anbukaci Al, ummar kasannan da suyi karatun ta nutsu bisa yadda Alamuran rayuwa suke gudana musanman,a wannan lokaci Domin kuwa Wanda ya halicce mu ALLAH Madaukakin Sarki ya kasance ya siffantu da Tausayi kuma mai tausayawa Bayinsa ta kowacce fuska.
Saboda haka nema ya arawa bayinsa, wannan siffa domin shugabanni su tausayawa wadanda suke mulka,suma wadand ake mulka su tausayawa masu mulkin nasu, wannan batun na MALAM Usman Muhammad Mal sheik Babban limamin masallachin JUMA, A na Abubakar Saddiq dake sheka Hanyar Dantsinke shine yayi wannan Bayaninne a cikin hudubarsa ta JUMA,a da ya gabatar a yau.
Mal sheik Usman ya bayyana cewar hakkine akan wadanda ya wajaba su kare kima da Daraja da mutuncin wadanda suke mulka Domin yau
Anyi Biris da halin da Al, umma suke ciki na rashin tsaro da rashin abinci da rashin aikin yi.
Mal sheik Usman yace yakamata l,umma suyi karatun ta nutsu bisa yadda ana ji ana gani ana samun matsaloli a jihohin kasannan, kwanannan aka sace mutum da iyalan sa a Kaduna baya ga yadda ake samun kashe -kashen rayuka a jihohin sokoto zamfara katsina kebbi.
Kasann tana bukatar a tausaya talaka bisa yadda masu satar mutane suka hana noma a gonaki,wasu garuruwan ma mazauna garin sun tsare saboda tsoron mahara da ke zuwa suci zarafinsu a yankin .
Sheik Usman ya karanto Ayoyin kur,ani Maigirma da Hadisan Annabi Muhammad tsira da Aminci su tabbata a gareshi akan kowanne shugaba ya tausayawa talakan da ake mulka.
Mal sheik Usman ya ce kowa ya sani ALLAH ya nann a madakata yana jiran kowa dukkan Wanda ya tausayawa talakan da ake mulka Shima ALLAH zai tausaya masa.
Akarshe sheikh USMAN yaja hankalin musulmi da su tashi suyi Sàllah cikin Dare domin kai kuka ga ALLAH ya maganta.
