JIGAWA TA KULLA ƘAWANCE DA WATA KAMFANIN MASAR A FANNIN KIRKIRAR SHUKA A ƊAKIN GWADAWA
Jihar Jigawa na shirin ƙulla muhimmiyar yarjejeniya ta haɗin gwiwa da wata fitacciyar kamfanin bincike da bunƙasa harkokin shuke-shuke da ke ƙasar Masar, EFC Plants, domin amfani da fasahar zamani ta kirkirar shuke-shuke a cikin ɗakin gwaje-gwaje (Plant Tissue Culture Technology).
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jagoranci wata tawagar ƙwararru ta gwamnatin jihar zuwa birnin Alkahira domin fara tattaunawa kan wannan haɗin gwiwa, wanda aka tsara zai taimaka wajen haɓaka noman dabino da dankalin Irish (Irish Potato) a jihar.
Wannan ziyarar fasaha da zuba jari na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na sauya fasalin harkar noma ta hanyar amfani da kimiyya da fasahar kere-kere, inganta samar da ingantattun tsirrai marasa cututtuka, ƙara yawan amfanin gona da kuma jawo hankalin masu zuba jari masu zaman kansu zuwa muhimman sassan harkar noma.
A yayin ziyarar, Gwamna Namadi da tawagarsa sun duba cibiyoyin EFC Plants da ke gudanar da bincike kan fasahar ƙwayoyin tsirrai da fasahar kere-kere. Cibiyoyin sun haɗa da manyan gidajen noma masu kula da yanayi, wuraren adana tsirrai masu sanyi da za su iya ɗaukar har zuwa tsirrai miliyan shida, dakin binciken cututtukan tsirrai, wuraren tsaftacewa da shirya tsirrai, da kuma ɗakunan musamman na bunƙasa da shigar da tsirrai.
Tawagar ta kuma samu cikakken bayani kan matakan samar da tsirrai ta hanyar Tissue Culture, tun daga zaɓe da gwajin asalin tsiro a dakin gwaje-gwaje, zuwa yawaitar ƙwayoyin tsiro, bunƙasawa, fitar da saiwoyi, daidaita tsirrai da yanayin waje, kula da su a gidajen noma, adanawa da kuma shirya su domin rabawa ko sayarwa a kasuwa.
Haɗin gwiwar da ake shirin kullawa zai mayar da hankali ne kan kafa da kuma bunƙasa fasahar Plant Tissue Culture a Jihar Jigawa, inda za a fara da dabino da dankalin Irish.
Ana sa ran wannan haɗin gwiwa zai samar da damar musayar fasaha, horas da ƙwararru, haɗin gwiwar bincike da kuma samar da ingantattun tsirrai marasa cututtuka masu yawan amfanin gona a cikin jihar.
Da yake magana kan shirin haɗin gwiwar, Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa manufar gwamnatin jihar ba ita ce kawai sayen tsirrai ba, illa kafa cikakkiyar alaƙar fasaha da zuba jari.
Gwamnan ya ce: “Haɗin gwiwarmu da EFC Plants zai wuce sayen kayan dasa shuki. Muna neman cikakkiyar alaƙa da za ta samar da musayar fasaha, bunƙasa ƙwarewar ‘yan jihar, haɗin gwiwar bincike, zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu da kuma samar da ingantattun tsirrai a kasuwanci a Jihar Jigawa.”
Ya ƙara da cewa amfani da fasahar Tissue Culture da fasahar kere-kere a harkar noma zai taimaka wajen magance matsalolin da manoma ke fuskanta wajen samun ingantattun kayan dasa shuki, tare da ƙarfafa matsayin Jigawa a fannin noma mai dogaro da fasahar zamani.
Gwamna Namadi ya ce: “Ta hanyar saka jari a fasahar Tissue Culture da fasahar kere-kere a harkar noma, za mu inganta damar manoma wajen samun ingantattun tsirran dabino da dankalin Irish, ƙara yawan amfanin gona, rage dogaro da kayan dasa shuki da ake shigo da su daga ƙasashen waje, tare da mayar da Jihar Jigawa cibiyar noma mai amfani da fasahar kere-kere a Najeriya.”
Jihar Jigawa na da muhimmiyar damar bunƙasa noman dabino saboda yanayin busasshen ƙasar da ya dace da noman dabino, da kuma yawan filayen ban-ruwa, al’adar noma da ta kafu a jihar da kuma kusancinta da manyan kasuwannin cikin gida.
Haka kuma, jihar na da damar faɗaɗa noman ingantaccen dankalin Irish ta hanyar amfani da tsirrai marasa cututtuka da kuma sabbin fasahohin noma.
A ƙarƙashin shirin haɗin gwiwar, gwamnatin Jihar Jigawa za ta yi aiki tare da EFC Plants, hukumomin jihar da abin ya shafa, kamfanoni masu zaman kansu daga Najeriya da sauran masu zuba jari masu sha’awar aikin.
Matakan farko da za a ɗauka sun haɗa da gudanar da cikakken binciken fasaha, nazarin yiwuwar aiwatar da aikin, zaɓen wurin da ya dace, tsara tsarin kasuwanci da aiwatar da aikin mai inganci, da kuma tattaunawa kan tsarin haɗin gwiwar da ya dace.
Tawagar da Gwamna Namadi ya jagoranta ta ƙunshi Dr. Suleiman Rufai Babura, Darakta-Janar na Jigawa Research Institute; Dr. Saifullahi Umar, Darakta-Janar na Jigawa Agricultural Transformation Agency; da Dr. Abubakar Isa Bamai, Babban Daraktan Natay Agro Limited.
Ziyarar Alkahira na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin Jihar Jigawa na shigo da kimiyya, fasaha da zuba jari masu zaman kansu cikin harkar noma, da nufin ƙara yawan amfanin gona, ƙarfafa samar da abinci, da samar da damammaki a harkar noma ta kasuwanci, sarrafa amfanin gona, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa fitar da kayan amfanin gona zuwa ƙasashen waje.
Related Posts
Add A Comment
