HON DOGUWA YA ROKI AFUWAR GWAMNAN JIHAR KANO, BISA ADAWA TA MAKANTA DA MUKAYI.
Shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa Wakilin kananan hukumomin tudun wada da Doguwa a majalisar kasa, ya nemi afuwar Gwamnan Jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf ne yayin taron kaddamar da Mai neman kujerar Dan Majalisar Dattawa na yankin kano ta kudu, wato Suleman Abdurrahman kawu Sumaila Wanda aka gudanar a filin wasa dake yankin masarautar Rano.

Hon Doguwa yace yayi Nadama bisa irin yadda ya yiwa Gwamnan Jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf Adawa siyasar da jayaya da nayi dakai abisa rashin sanin waye Kai,
ka nuna min Kai Gwamna ne Shugaba Mai Adalci,,
Lokacin da muke adawar siyasa da Kai da Banbarama da mukayi wannan bai hana idan kazo neman Dan takara Mai Inganci ka yarda kabani dama ajam, iyyar Apc wadda taka ce Kai kadai a Jihar kano.
Hon Alhassan Ado Doguwa ya karkare jawabin nasa da yin kira ga Gwamnan kano da ya yiwa Allah da manzansa ya mayar da masarautar Rano ta koma masarauta Mai Darajar ta daya, Kamar yadda take Abaya
