Kotu ta Tsare Direban Matar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Kan Zargin Sace Mata Gwala-Gwalai
Kotun majistare da ke zamanta a Nomansland ta bayar da umarnin tsare wasu mutane uku da ake zargi da satar gwala-gwalai, kuɗi da kuma wayar hannu na matar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da Abdullahi Usaini, inda ake tuhumarsu da laifuffuka uku da suka haɗa da haɗa baki wajen aikata laifi, sata da kuma karɓar kayan sata.
Mai gabatar da ƙara, Barrista Abubakar Ibrahim, ya bayyana wa kotu cewa Sulaiman Yakubu, wanda direba ne ga matar sarkin, ya shiga ɗakinta ba tare da izini ba tare da sace kayan ado da darajarsu ta kai kimanin naira miliyan 60, da kuɗi da kuma wayar hannu.
A cewar kotu, Sulaiman ya amsa laifinsa, yayin da sauran mutum biyun suka musanta zargin da ake musu.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga Afrilu domin ci gaba da shari’a, yayin da za a ci gaba da tsare su har sai sun cika sharuddan belin.
