Yanzu haka dai Yan Fashin daji a yankin Mandawa dake “Yanwaren Daji a Karamar Hukumar Tsare ta Jihar Zamfara sun cigaba da rasa rayukansu sakamakon barkewar cutar kwalara.
Idan dai za’a iya tuwa a kwanakin baya irin wannan annoba ta barke a sansanin da Yan Fashin dajin.
A yanzu haka dai wannan annoba na cigaba dayin musu dauki dai dai a guraren da suke zaune, inda suka fara neman a tayasu da addu’a tareda neman daukin Allah ya sawake musu.
Gwamnatin Tarayya Karkashin Shugaba Bola Ahmad Tinubu yasha alwashin ganin an kawae da irin wannan ta’addacin dake faruwa a sassan Kasar Nan daban daban.
A kwana kwanan ma Sai da Sai da Jami’an tsarin gadin giwwa suka samu nasarori akan wasu Yan Fashin dajin dake wasu sassan Jihar Zamfara da wasu yankunan Jihar Katsina.
Irin wadannan nasarori da Gwamnatin Tarayya ke samu akan harkar ta’addacin yana samuwa ne sakamakon addu’oi da jajircewar Jami’an tsaron Kasar.
