GWAMNA NAMADI YA YI ALKAWARIN CI GABA DA TAIMAKA WA MANOMA DA BUNKASA TATTALIN ARZIKI
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai tare da taimakon juna, yayin da ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ƙarfafa harkar noma da inganta tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan ya karɓi Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Haneem Muhammad Sanusi, a lokacin gaisuwar Hawan Bariki da aka gudanar a filin Durbar na Sir Muhammadu Sanusi da ke Dutse, a cikin shirye-shiryen bikin Eid-el-Fitr.
Ya bayyana ziyarar da Sarkin da sauran shugabannin gargajiya suka kai a matsayin wata dama ta yin tunani da godiya, yana mai cewa hakan ya ba da damar yaba haɗin gwiwar da ake yi wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaba da haɗin kai a faɗin jihar.
Gwamna Namadi ya ce ya samu ƙwarin gwiwa daga irin goyon bayan da cibiyoyin gargajiya suka nuna, musamman yadda suka yaba ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa a sassa daban-daban na masarautun jihar.
Haka kuma ya yaba wa al’ummar Jihar Jigawa bisa ci gaba da goyon bayan da suke bai wa gwamnatocin jiha da ta tarayya, yana mai cewa irin wannan haɗin kai yana da matuƙar muhimmanci wajen dorewar ci gaba.
“Mu a matsayin gwamnati, za mu ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba ga al’ummarmu, musamman marasa galihu. Hankalinmu kullum yana kan talakawan Jihar Jigawa,” in ji shi.
Dangane da ƙalubalen da manoma ke fuskanta, gwamnan ya amince cewa da dama daga cikinsu sun yi asara a ‘yan kwanakin nan, amma ya tabbatar da cewa gwamnatocin tarayya da ta jihar sun san halin da ake ciki kuma suna aiki domin samar da mafita.
“Noma shi ne babban jarin al’ummar Jihar Jigawa. Mun san halin da noma yake ciki a ƙasar nan; mutane na noma amma suna yin asara ba tare da riba ba. Amma ina so in tabbatar wa jama’armu cewa wannan matsala ce ta ɗan lokaci. A matsayinmu na gwamnati, muna nazarin hanyoyin da za su tabbatar manoma suna cin riba daga aikinsu.”
Ya bayyana cewa an riga an tsara hanyoyin taimaka wa manoma kafin zuwan noman rani, domin su koma gonakinsu cikin kwarin gwiwa tare da ƙara yawan amfanin gona.
“Daga wannan kakar noma da za ta fara a wannan shekara, insha Allahu, za mu kawo tsare-tsaren da za su taimaka wa ƙananan manoma. Don haka muna kira da a yi haƙuri yayin da za mu shiga kakar noma; da yardar Allah za mu ba da tallafi domin taimaka wa manoma.”
“Abu ɗaya tabbatacce ne; idan muka ƙi noma, ba za a samu abinci ba. Idan aka samu ƙarancin abinci, farashinsa zai tashi, kuma idan farashin ya tashi, za mu shiga wahala.”
“Mun san abin da ke jefa manoma cikin ƙunci; tsadar taki da sauran abubuwa. Da yardar Allah, za mu kawo sauƙi domin talakawa su iya gudanar da noma yadda ya kamata.”
Game da ƙarin farashin man fetur da aka samu a baya-bayan nan, Gwamna Namadi ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fara ɗaukar matakai domin rage tasirin hakan ga al’umma, ciki har da ƙoƙarin rage kuɗin sufuri ta hanyoyi daban-daban.
“Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarce ni da in sanar da al’ummarmu cewa an samu ƙarin farashin mai ne sakamakon rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya. Wannan ƙari zai ɗora nauyi a kan al’umma. Amma shugaban ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ɗauki matakan rage wannan nauyi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa waɗannan matakai, musamman ta hanyar taimaka wa manoma domin rage tasirin da hakan zai yi ga al’umma.
Gwamnan ya kuma yi amfani da wannan dama wajen ƙarfafa gwiwar al’umma su shiga cikin rajistar masu kaɗa ƙuri’a da ake ci gaba da yi, yana mai jaddada cewa katin zaɓe na da muhimmanci wajen shiga cikin tsarin dimokuraɗiyya.
“Muna kira ga kowa ya fita ya yi rajista; waɗanda ba su yi ba su je su yi; waɗanda katinsu ya lalace su je su sabunta; waɗanda suka canza matsuguni su je su sabunta bayanansu.
“Wannan katin zaɓe shi ne ƙarfinku. Idan kuna da katin zaɓe kuma Umar Namadi bai yi muku adalci ba, za ku iya kalubalantarsa a akwatin zaɓe. Duk wani zaɓaɓɓen shugaba da bai yi muku abin da ya dace ba, ku yi amfani da wannan kati wajen sauya shi.”
Related Posts
Add A Comment
