JIGAWA TA ƊAUKI SABUWAR DABARA TA RUWA DON MAGANCE RIKICIN MANOMA DA MAKiyaya
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta bullo da sabuwar dabara mai inganci domin magance matsalolin tsaro da suka shafi iyakokin ƙasa, musamman hijirar dabbobi daga Jamhuriyar Nijar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga Cibiyar Kula da Bayanai ta Sirri (Strategic Intelligence Management Institute – SIMI), ƙarƙashin jagorancin Ambasada M.D. Aliyu, a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
A jawabinsa, Gwamna Namadi ya ce shigowar shanu da rakuma daga Jamhuriyar Nijar, musamman a lokacin tsananin fari, na janyo cunkoso ga albarkatun ƙasa tare da haddasa rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya.
Sai dai ya ce gwamnatin jihar ta samar da wata sabuwar hanya ta magance wannan matsala, ta hanyar samar da wuraren ruwa a ƙetaren iyaka domin taimakawa makiyaya su zauna can na tsawon lokaci kafin su shigo Najeriya.
Ya ce: “Mun ƙirƙiri wannan dabara ta samar da ruwa a waje da iyaka domin makiyaya su ci gaba da zama a can har sai manoma sun kammala girbin amfanin gonarsu. Wannan mataki ya rage rikice-rikice sosai tare da inganta zaman lafiya.”
Gwamnan ya ƙara da cewa wannan shiri na nuna yadda jihar ke amfani da dabarun rigakafi da bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da al’umma wajen magance matsalolin tsaro maimakon jiran su faru.
Ya jaddada cewa zaman lafiyar da ake samu a Jigawa, duk da kusancinta da yankunan da ke fama da matsaloli, ya samo asali ne daga manufofi masu kyau, haɗin kai da jami’an tsaro, da kuma hulɗa da al’ummomin kan iyaka.
Gwamna Namadi ya kuma bayyana Jigawa a matsayin jiha mai muhimmanci a tsarin tsaron ƙasa na Najeriya, yana mai cewa irin waɗannan sabbin dabaru na cikin gida na da matuƙar tasiri wajen magance ƙalubalen tsaro da suka shafi ƙasashe da dama.
Ya ba tawagar tabbacin cikakken haɗin kai daga gwamnatin jihar, tare da fatan bincikensu zai ƙara inganta dabarun tsaro a Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya.
Tun da fari, Ambasada M.D. Aliyu ya yabawa gwamnatin Jigawa kan karɓar baƙi da kuma dabarun da take amfani da su wajen tsaro, yana mai cewa an zaɓi jihar ne saboda irin yanayin iyakokinta da kuma nasarorin da take samu a fannin tsaro.
Ya bayyana cewa ziyarar na daga cikin wani shiri na horaswa na Strategic Intelligence Management Course II, wanda aka tsara domin bai wa manyan jami’an tsaro da leƙen asiri damar fahimtar matsalolin tsaro a zahiri da kuma hanyoyin magance su.
A cewarsa, tattaunawar da za su yi da masu ruwa da tsaki a Jigawa za ta taimaka wajen fahimtar matsaloli kamar shige da fice ba bisa ƙa’ida ba, safarar kayayyaki, da sauran laifukan da suka shafi ƙasashe da dama, tare da samar da shawarwari masu amfani ga manufofin gwamnati.
Ya ƙara da cewa wannan shiri zai taimaka wa mahalarta wajen fahimtar ƙalubalen tsaron iyakoki da suka haɗa da safarar makamai, miyagun ƙwayoyi, fataucin mutane, da sauran manyan laifuka na ƙasa da ƙasa.
Related Posts
Add A Comment
