Shugaban yan majalisun Arewacin nijeriya Babban jami in yakin neman zaben shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu a na Arewa maso yamma bisa majalisar kasa Rt Hon Alhassan Ado Doguwa OON. Ya Sake Sauke Kabakin Arziki a Makarantar Daɗin Kowa Science and Mathematics Primary School dake Karamar Hukumar Doguwa
Hon Alhassan Ado ya bayar da gudunmawar Naira Miliyan Ashirin (N20,000,000) Ga Makarantar Primary ta DAƊIN KOWA PRIMARY SCHOOL Makarantar da shi kansa YaYi Karatun Primary a Cikinta.
Wannan kudi za a yi amfani Dasu ne wajen:-
1. Gyaran azuzuwa baki daya
2. Saka sabbin kujerun karatu ga dalibai
3. Gina sabbin bandakuna (makewayi) na zamani ga Malamai da Dalibai
4. Gina sabbin ofisoshin Malamai
Mai Girma JAGORA Rt Hon Alhassan Ado Doguwa Yana Tareda Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Hon Umar Haruna Doguwa da Shugaban Karamar Hukumar DOGUWA Hon Abdulrashid Rilwan Doguwa da Alhassan Muhammad Oko Riruwai.
Wannan shine shugaba mai kishin kasa da kishin ilimi

Al, umma yankin sun nuna farm cikin su bisa yadda rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya ke baiwa Ilimi gudummawa ta ko wacce fuska
Ko a makon da ya gabata ya baiwa kungiyar Daliban karamar hukumar Tudun wada dana Doguwa miliyoyin kudi Domin sanin mahimmancin Ilimi,baya ga sayawa Daliban da ke karatu a kwalejin Sa,adatu Rimi gida sukutum a yankin karamar hukumar kumbotso,domin sukaka musu,tare da baiwa Daliban kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa Tallafin karatu wato scholarship.
