tuni dai shirye -shiryen Bikin yayi nisa,kamar yadda shugaban kwamitin yada yada labarai na shirin bikin Dr, Gwani Faruk Umar ya bayyana wa jaridar muryar Arewa A yau.com.

Gwani Faruk Umar yace an kafa kwamitittuka domin samun Nasarar bikin cikar kwalejin shekaru 100.
Kwamitin sun hada da kwamitin yada labarai,da kwamitin kudi da kwamitin shirye -shirye da na tsare -tsare da makamantansu.
Tuni dai shugaban kungiyar Daliban makarantar na kasa Ajiyan kazaure Dr,Nu,uman Barau Danbatta,d da makaman Bichi Alh Isyaku Umar Tofa ke jagorancin zaman yadda za,aga angudanar da Bikin cikar kwalejin RUMFA,shekaru 100 .

Kwalejin RUMFA da bata da Sa, a. Wajen fitar da Dalibai da sukayi shura a Duniya,ta fuskar mulki da fasahar zamani da mukamai daban -Daban a fannin Ilimi da kasuwanci da sauran sassa na rayuwar Dan, Adam.
Kwalejin Rumfa makarantar tana da Babban tarihi wanda baza a manta da shiba, jihar kano na Alfahari da wannan babbar makarantar.
