“’Yan sanda ba su da hurumin raka mutane wajen karɓar filaye” — IGP Egbetokun
Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda ba su da hurumin raka mutane ko kamfanoni wajen karɓar ko kwace filaye a kasar nan.
IGP Egbetokun ya yi wannan jawabi ne a yayin da ake tattaunawa kan batun rikicin fili da ya faru a Abuja, wanda ya shafi Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
A cewarsa, jami’an da suka raka irin waɗannan ayyuka ba tare da umarnin doka ba suna yin hakan ne da kansu, kuma za su ɗauki alhakin duk abin da ya faru.
“Idan wani jami’in ‘yan sanda da ya shiga irin wannan tafiya ya shiga wani hali, to shi kaɗai ke da alhakin abin da ya same shi,” in ji IGP Egbetokun.
Ya ƙara da cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda, amma ba za ta yarda jami’anta su zama kayan aiki wajen lamurran da ba su da tushe na doka ba.

