Gwamna Namadi Ya Yafewa Fursunoni 12 a Jihar Jigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya bai wa fursunoni 12 da aka yankewa hukunci afuwa ta jiha, a matsayin nuna jin ƙai da kuma la’akari da ruhin watan Ramadan da kuma bikin Sallah mai zuwa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Bello Abdulkadir Fanini, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce an dauki wannan mataki ne bisa shawarar Kwamitin Ba da Shawara kan Afuwa na Jihar Jigawa, kamar yadda doka ta tanada a sashe na 5(1) na dokar Kwamitin Afuwa (Cap A2) ta shekarar 2012.
An aiwatar da wannan afuwa ne karkashin ikon da sashe na 212(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (da aka gyara) ya bai wa gwamna, da nufin inganta sulhu da kuma mayar da wadanda aka yafe wa cikin al’umma.
Ga sunayen wadanda suka ci gajiyar afuwar:
Ibrahim Adamu Isa
Sa’idu Umar
Adamu Musa
Habibu Musa
Yusuf Ahmed
Shu’aibu Adamu
Abdullahi Ya’u
Yahaya Jana’u
Abdul Hamisu
Garba Miko
Salisu Isa
Aliyu Ibrahim
Barista Fanini ya bayyana cewa wannan mataki na nuna irin kudurin gwamnatin jihar wajen karfafa zaman lafiya da kyautata zamantakewa a cikin al’umma.
Ya kuma bukaci wadanda aka yafe wa su ci gaba da nuna kyawawan halaye kamar yadda suka yi a lokacin da suke tsare, tare da gujewa sake aikata laifuka.
Kwamishinan ya kara da cewa, “Wadanda aka yafe wa sun nuna hali na gari kuma saura watanni kadan su kammala wa’adin hukuncin da aka yanke musu.”
