Wani sako Mai dauke da sa hannun , Hon. Alhassan Ado Doguwa, ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, 13/03/2026, bayan kammala taro da muka gudanar na rabon tallafin kayan azumi da na Sallah ga al’ummar ƙaramar hukumar Tudun Wada mata da maza.
Amma daga baya na samu labarin cewa wasu bata gari sun yi yunƙurin tayar da tarzoma a wurin rabon kayan, lamarin da ya yi sanadin rasuwar wani jami’in tsaro na Civil defence.
Ina miƙa ta’aziyyata ga Hukumar tsaro ta Civil Defence, iyalansa, da kuma al’ummar ƙaramar hukumar Tudun Wada baki ɗaya. Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa. Ameen.
Zan yi amfani da wannan dama nayi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka haddasa wannan tashin hankali, tare da ɗaukar matakin da ya dace a kansu bisa doka.
A ƙarshe, ina jan hankalin waɗanda suke yaɗa labaran ƙarya da kalaman batanci da suke alakanta ni kai tsaye da wannan abinda ya faru cewa za mu ɗauki dukkan matakan doka da suka dace domin kare mutuncinmu da na al’ummar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada.
Shi kuma Allah Ya jikansa Ya masa rahama. Ameen.
