: Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance Murtala Sule Garo don zama mataimakin Gwamna
Majalisar dokokin jihar Kano ta kammala tantance Hon. Murtala Sule Garo, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa a matsayin Mataimakin Gwamna.
Sakataren yaɗa labarai na majalisar dokokin jihar Kano, Kamaludeen Sani Shawai ne ya tabbatar da hakan cikin wata gajeriyar sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Acewarsa, kwamitin da Mataimakin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Muhammad Bello Butu Butu ke jagoranta, zai gabatar da rahotonsa ranar Litinin domin amincewa ta ƙarshe.
