Da yake jawabi a wani taro kan tattalin arziƙi a birnin Legas, Muhammadu Sanusi ya yi gargaɗin cewa rashin alkilta kuɗi ka iya zagwanye cigaban da ake tunani za a samu sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙin da Najeriya ta yi.
Sarki Sanusi ya soki yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da ciyo bashi duk da janye tallafin man fetur
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya soki yadda gwamnati ke ci gaba da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur a ƙasar.
Sanusi ya bayyana hakan ne a wani taron shekara-shekara na TheNiche Annual Lecture 2026 da aka gudanar a Legas, inda ya ce bai dace a a dena bada tallafin mai ba amma a ci gaba da karɓar bashi ba tare da ganin amfanin hakan ba.
Ya ce cire tallafin ya zama dole saboda tsadar da yake haifarwa, tare da nuna cewa yanzu Najeriya ta fara tace mai a cikin gida maimakon shigo da shi daga waje, lamarin da ya kamata ya inganta tattalin arziki.
Sai dai ya jaddada cewa ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan daidaita harkokin kuɗi, yana mai tambayar dalilin da ya sa ake ci gaba da karɓar bashi duk da cewa an samu kuɗaɗen da ake kashewa a baya kan tallafi.
Sanusi ya kuma kare wasu muhimman sauye-sauye kamar cire tallafi da sassauta tsarin canjin kuɗi, amma ya nuna damuwa kan yadda aka aiwatar da su, yana cewa rashin tsaurara tsarin kula da yawan kuɗin da ke yawo ya janyo faduwar darajar naira.
Ya ƙara da cewa cire tallafin ya zama tilas ne a lokacin da kusan dukkan kudaden shiga na gwamnati ke tafiya wajen biyan bashin ƙasa, amma ya gargadi cewa dole ne a aiwatar da manufofi cikin tsari domin kauce wa ƙarin matsin tattalin arziki.
