Kotu Ta Ba da Umarnin Kama Hon. Idris Dan Kawu kan Zargin Badakalar Naira Miliyan 77
Wata Kotun Magistrate da ke Bwari, Dutsen Alhaji a Abuja ta bayar da umarnin kama Hon. Idris Dan Kawu bisa zargin hannu a wata badakalar kuɗi ta sama da naira miliyan 77.
Rahotanni sun nuna cewa umarnin kotun ya biyo bayan karar da wani kamfani mai suna BAMZ Multi Essential Services ya shigar ta hannun lauyansa, Barrister Ahmad Umar Faruk.
Kamfanin ya yi zargin cewa an karɓi kuɗaɗen har naira miliyan 77,035,069 domin wani aikin samar da hasken rana na solar da aka yi alkawarin bayarwa, amma har zuwa yanzu ba a aiwatar da aikin ba.
A cewar lauyan kamfanin, an tura kuɗin ne a ranar 18 ga watan Satumban 2025 ta hannun hadimin Hon. Dan Kawu, Ismail Yakubu Abubakar.
Barrister Ahmad Umar Faruk ya ce bayan kuɗin sun shiga asusun Ismail Yakubu Abubakar, wanda ake zargi ya sanya hannu kan takardar tabbatar da karɓar kuɗin.
Ya ƙara da cewa tun farko Hon. Idris Dan Kawu ya shaida musu cewa akwai aikin solar da zai bai wa kamfanin, amma sai aka buƙaci su bayar da kaso 10 cikin 100 na kuɗin kafin a fitar musu da takardar bayar da aikin.
Sai dai lauyan ya ce bayan cikar duk sharuddan da aka gindaya musu, ba a samu aikin ba kuma ƙoƙarin da suka yi na ganin an dawo musu da kuɗinsu bai yi nasara ba.
Rahoton ya nuna cewa kotun ta bayar da umarnin kama wanda ake zargin domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake masa.
Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin hadimin Hon. Dan Kawu, Ismail Yakubu Abubakar, ya ci tura, domin wayarsa na nuna “line busy” ko kuma a kashe take.
Haka kuma an tura masa saƙon neman martani kan lamarin, amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai bayar da wata amsa ba.
Jaridar mu za ta ci gaba da bibiyar shari’ar tare da wallafa duk wani martani daga bangaren wanda ake zargi domin tabbatar da adalci da daidaito a aikin
