Kakakin Majalisar Wakilai Ya Bukaci Sakamakon Bincike Kan Mutuwar Wadanda Ake Zargi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba
KAKAKIN MAJALISAR WAKILAI ABBAS YA BUKACI SAKAMAKON BINCIKE KAN MUTUWAR MASU HAƘAR MA’ADINAI DA AKA KAMO
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya yi kira da a fitar da sakamakon binciken da ake gudanarwa kan mutuwar wasu mutane da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, waɗanda suka mutu a hannun jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC).
Kakakin Majalisar ya bayyana cewa, sakamakon binciken zai taimaka wajen gano matsalolin da suka haifar da lamarin, da kuma samar da hanyoyin magance su domin hana sake faruwar irin wannan al’amari a nan gaba.
A cikin wata sanarwa, Abbas Tajudeen ya ce ya kamata binciken ya duba batutuwan da suka shafi cunkoso a cibiyoyin tsare mutane, ƙa’idojin gudanar da ayyukan jami’an tsaro, haƙƙoƙin waɗanda ake zargi, da kuma walwalar mutanen da ke tsare a hannun hukumomin tsaro.
Ya kuma jaddada muhimmancin gudanar da binciken cikin gaskiya, bayyananniyar hanya da kuma ɗaukar alhaki, yana mai cewa dole ne a tabbatar da an yi wa waɗanda suka mutu adalci, sannan al’umma ma ta ga cewa an yi adalcin.
A cewar Kakakin Majalisar, hakan zai taimaka wajen kwantar da hankalin jama’a da kuma dawo da amincewarsu da tsarin bincike da tabbatar da adalci.
Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, da kuma gwamnatin Jihar Neja bisa wannan mummunan lamari.
Related Posts
Add A Comment
