Mai sharhi akan Al,amuran da suka shafi Tattalin farfesa Garba Ibrahim Sheka,ya bayyana cewar sayar da hannun jari na kamfanin mai na Dangote zai bada dama ga Al, ummar kasa nijeriya,bisa la,akari da baiwa kowa damar saka hannun jari, yayinda a gefe guda kuma Talak da yake can kasa zai fuskanci matsi da kuncin rayuwa.
Farfesa sheka yace ,abaya wannan matatar mai tasha fama da fadi tashi da gwagwagwa,kai harma da masu yunkurin sai an ga bayan matatar mai din, bisa wasu dalilai na rashin cigaba.
Yayinda Alh Dr,Aliko Dangote yayi dogon Nazari wajen cewar bari ya saki wasu daga cikin hannun jari na kamfanin mai din,domin l kasa suma su amfana,,hanyar da yake ganin cewar zata bille , sakamakon tsangwama da bakin ciki da ake nunawa matatar mai.
Sai dai kuma daga kan masu kudi na sama,zuwa matsakaita sune zasu sha lagwadar wannan tsarin na sayar da hannun jari,yayinda talakawa na can karshe zasu fuskanci matsi na tattalin Arziki, musanman ma idan kana da motar hawa,da ke shan manfetur na dubban Naira,ga Abinci ga sauran harkokin yau da kiullum da ke bukatar kudi.,wanda hakan ka iya zama wajibi a rage tsayi domin kare dukan matsalar tattalin Arziki dake yunkurin kai Al, umma kasa.
Duk wanda ya sayi jarin mai na Dangote a kowanne lokaci yaga motar dakon mai ta Dangote nan ne zai yi Tinkaho cewar shima fa akwai kasonsa a ciki,koda kuwaefarashin mai na cigaba da karuwa a gidajen mai .
Rashin tabbas akan farashin mai ko Kari ko ragi na iya zama abin tsoro a wajen talaka,na kasa.
Babban abinda zamu jira shine yadda idan aka kammala sayar da hannun jarin kamfanin mai na Dangote yadda kasuwar mai zata zama,in ba a gatari ba a kota.
Zanu cigaba
