Close Menu
  • Home
  • Kasuwanci
  • Nishadi
  • Features
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Karin Wasu
    • Noma da Kiwo
    • Sauyin Yanayi
    • Fasaha
Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
Facebook X (Twitter) Instagram
MURYAR AREWA A YAU
Subscribe
  • Home
  • Kasuwanci

    GWAMNAN JIHAR KANO ALH ABBA KABIR YUSUF YA SAUKE KWAMISHINAN ZUBA JARI DA KASUWANCI, DAGA KAN MUKAMINSA

    March 26, 2026

    FILIN JIRGIN SAMAN DUTSE JIHAR JIGAWA ZAI DINGA KARBAR KAYA NA KAGO

    February 23, 2026

    Zulum Leads Fintiri, Buni to Meet New World Bank Director

    November 14, 2025

    Gwamnatin Najeriya ta roki jama’a su rage cin ganda (ponmo) kada kamfanin sarrafa fata na kasar ya durkushe

    November 14, 2025

    STANDARD ORGANIZATION OF NIGERIA AND FEDERAL MINISTRY OF TRADE ARE GOING TO WORK TOGETHER

    November 8, 2025
  • Nishadi

    WANI : MAGIDANCI MAI MATA BIYU A BAUCHI, YA KASHE DAN ACABA DON SAMUN KUDIN KARA AUREN MATA TA UKU

    October 22, 2025

    Qausain TV appoints Adam A. Zango as Director-General

    October 8, 2024

    Young Jonn Sets To Thrill Fans With Electrifying Performance In Abuja

    September 29, 2024

    Why Bobrisky was separated from other inmates – Prison experts

    September 27, 2024
  • Features

    GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ZATA BULLO DA SABBIN DABARUN WARWARE MATSALOLIN MANOMA DA MAKIYAYA,TARE DA TANTANCE KAN IYAKOKI

    April 14, 2026

    AN SHAWARCI MALAMAI DAKE GUDANAR DA DA, AWAH DA SU DINGA KARANTAR DA WADANDA AKA MUSULUNTAR DOMIN SU SAN ADDININ MUSULUNCI, INJI BARR, YAHYA IBRAHIM ALIYU R

    April 14, 2026

    GWAMNAN JIHAR JIGAWA MALAM UMAR NAMADI DAN MODI YA CE, ILIMI BABBAN JARI DOMIN CIGABAN JIHAR JIGAWA,DAMA KASA BAKI DAYA

    April 12, 2026

    JIGAWA STATE IS A WRONG PLACE TO COMMIT CRIME AS AFFIRMED BY THE DECISIONS OF THE SUPREME COURT OF NIGERIA.

    April 11, 2026

    YAN FASHIN DAJI NA FAMA DA ANNOBAR AMAI DA GUDAWA, HAR TA YI AWON GABA DA WASU DAGA CIKIN SU ZUWA LAHIRA

    April 9, 2026
  • Labarai

    JIGAWA A ROLE MODEL FOR HEALTH SECTOR REFORMS IN NIGERIA – ZAMFARA PS PUBLIC SERVICE OFFICE

    April 1, 2026

    AN TSARE WANI DIREBAN MOTAR MATAR SARKI BISA ZARGIN SATAR GWALA – GWALAI NA MILIYOYIN KUDI MASU TSADAR GASKE

    April 1, 2026

    CELEBRATING A VISIONARY LEADER r AT 74TH : DG DAN’AGUNDI FELICITATES PRESIDENT TINUBU ON HIS BIRTHDAY

    March 29, 2026

    KUNGIYAR TALLAFAWA MARAYU DA GAJIYAYYU TA YAHAYA IBRAHIM ALIYU CHARITY FOUNDATION TA MIKA SAKON TA, AZIYYA

    March 29, 2026

    EMIR BAYERO RALLIES NIGERIANS IN POWERFUL PRAYERS PRAYERS FOR FOR r PEACE , SECURITY AND ECONOMIC REVIVAL.

    March 23, 2026
  • Siyasa

    REJOINDER: THE FALLACY OF THE “COMMANDER AND THE BURDEN OF INTEGRITY

    April 5, 2026

    MATASAN JIHAR KANO SUNCE :-MURTALA SULE GARO NE YAFI CANCANTAR ZAMA MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KANO

    April 4, 2026

    HON ALHASSAN ADO DOGUWA, YACE WAJIBI NE AYI KYAKYKYAWAN SHIRI DOMIN TUNKARAR ZABEN SHEKARA TA 2027 DOMIN KUWA AKWAI GAGARUMAR MATSALA

    April 2, 2026

    GANDUJE PUSHES GARO FOR KANO DEPUTY GOVERNOR AS APC STAKEHOLDERS KICK AGAINST MOVE

    April 1, 2026

    AN BUKACI MAGOYA BAYAN SHEIKH IBRAHIM KHALIL DASU FITO RANAR ALHAMIS DOMIN TARBARSA, A FILIN JIRGIN SAMAN MALAM AMINU KANO

    April 1, 2026
  • Tsaro

    JIGAWA STATE IS A WRONG PLACE TO COMMIT CRIME AS AFFIRMED BY THE DECISIONS OF THE SUPREME COURT OF NIGERIA.

    April 11, 2026

    YAN FASHIN DAJI NA FAMA DA ANNOBAR AMAI DA GUDAWA, HAR TA YI AWON GABA DA WASU DAGA CIKIN SU ZUWA LAHIRA

    April 9, 2026

    KHADIJA ISAH THE 9 YEAR OLD VICTIM OF BRUTAL RAPE GOT JUSTICE .

    April 9, 2026

    GWAMNAN JIHAR JIGAWA MALAM UMAR NAMADI DAN MODI YA YI WA WASU MASU ZAMAN GIDAN GYARAN HALI AFUWA 12

    March 19, 2026

    GWAMNATIN JIHAR KANO TA DAUKI MATAKIN TSAURARA TSARO YAYIN SALLAR IDI DA ZA, A GABATAR NAN GABA KADAN DOMIN BIN DOKA DA ODA

    March 18, 2026
  • Wasanni

    Ndume Unity Cup 2025: Drama, Determination, and Dominance as Matchday 1 Unfolds.

    November 15, 2025

    MAGOYA BAYAN KUNGIYAR KWALLON KAFA TA KATSINA UNITED TA SUN RAUNATA YAN WASAN KUNGIYAR KWALLON KAFA TA BARAU FC TARE DA YIWA MOTOCIN BARAU FC ROTSE

    November 8, 2025

    NASARAR GIWA UNITED FILIN SUKUWA

    October 24, 2025

    new Kano-based football club, Bichi First FC, has appointed renowned journalist Muzammil Dalha Yola as its Media Officer.

    September 12, 2025

    Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Barau da Kano pillars Duk Na Y’aya”n Jihar kano ne Ba Na Mutum Daya bane – :Inji Adamu Abdullahi karkasara

    August 19, 2025
  • Karin Wasu
    1. Noma da Kiwo
    2. Sauyin Yanayi
    3. Fasaha
    4. View All

    GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ZATA BULLO DA SABBIN DABARUN WARWARE MATSALOLIN MANOMA DA MAKIYAYA,TARE DA TANTANCE KAN IYAKOKI

    April 14, 2026

    GWAMNAN JIHAR JIGAWA MALAM UMAR NAMADI YA YI ALKAWARIN CI GABA DA TAIMAKA WA MANOMA DA BUNKASA TATTALIN ARZIKI

    March 22, 2026

    GWAMNATIN JIHAR JIGAWA TA KADDAMAR DA KASHI NA UKU NA TALLAFAWA MA, AIKATAN GWAMNATI TA FUSKAR NOMA

    March 13, 2026

    GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ZATA HADA GWIWA DA NDDB NA KASAR INDIA DOMIN SAMAR DA MADARA DA BUNKASA KIWON SHANU

    March 10, 2026

    MALIKAWA GARU :- PLANT A TREE TODAY TO FIGHT DESERTIFICATION

    October 16, 2025

    Zulum commissions housing complex for teachers in Mafa

    October 7, 2025

    NiMet Predicts Three-day Thunderstorm, Downpour Nationwide

    October 14, 2024

    NiMET Predicts Three-Day Thunderstorms From Monday

    October 1, 2024

    Zulum: Borno begins export of plastic materials

    October 30, 2025

    Zamkah Technologies Has Signed MOU With Institute For Peace and Conflict Resolution (IPCR)

    September 9, 2025

    Digital Age: How Technology Impacts Modern Marriage

    September 29, 2024

    Artificial Intelligence will replace unskilled workers – Daily Trust

    September 27, 2024

    GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ZATA BULLO DA SABBIN DABARUN WARWARE MATSALOLIN MANOMA DA MAKIYAYA,TARE DA TANTANCE KAN IYAKOKI

    April 14, 2026

    AN SHAWARCI MALAMAI DAKE GUDANAR DA DA, AWAH DA SU DINGA KARANTAR DA WADANDA AKA MUSULUNTAR DOMIN SU SAN ADDININ MUSULUNCI, INJI BARR, YAHYA IBRAHIM ALIYU R

    April 14, 2026

    GWAMNAN JIHAR JIGAWA MALAM UMAR NAMADI DAN MODI YA CE, ILIMI BABBAN JARI DOMIN CIGABAN JIHAR JIGAWA,DAMA KASA BAKI DAYA

    April 12, 2026

    JIGAWA STATE IS A WRONG PLACE TO COMMIT CRIME AS AFFIRMED BY THE DECISIONS OF THE SUPREME COURT OF NIGERIA.

    April 11, 2026
MURYAR AREWA A YAU
Home » WANI : MAGIDANCI MAI MATA BIYU A BAUCHI, YA KASHE DAN ACABA DON SAMUN KUDIN KARA AUREN MATA TA UKU

WANI : MAGIDANCI MAI MATA BIYU A BAUCHI, YA KASHE DAN ACABA DON SAMUN KUDIN KARA AUREN MATA TA UKU

By Ali MuhammadOctober 22, 2025 Nishadi 5 Mins Read
police
Share
Facebook Twitter Email Telegram WhatsApp

WANI : MAGIDANCI MAI MATA BIYU A BAUCHI, YA KASHE DAN ACABA DON SAMUN KUDIN KARA AUREN MATA TA UKU

 

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta kama wani magidanci mai Sana’ar sayar da kayan marmari a Bauchi, saboda kashe dan acaba tare da dauke mashin dinsa don ya sayar ya samu kuɗin biyan sadakin ƙara auren mata ta uku.
Rundunar Ƴan sanda ta Jihar Bauchi ta sanar da kama mutumin mai suna Mamuda Zakaria Yau, mai shekaru 30 a duniya bisa zargin sa da caka wuƙa wa Basiru Mohammed mai shekaru 25 a duniya wanda ya ke sana’ar Achaɓa a cikin garin Bauchi.
Kamar yadda maj laifin ya shaidawa ‘Yan sanda cewa ya hau acaban daga shataletalen dogon yaro zuwa bayan tsohon airport a kan naira 600. amma da suka je wajen da babu mutane sai ya burma masa wuka a hau mashin ya kara wuta.
Jami’in hulda da Jama’a na Rundunar yan ‘sandan jihar Bauchi CSP Ahmad Muhammad Wakil a nasa karin bayani cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce a ranar Alhamis 16/10/2025 da misalin karfe 9 na dare wani mai suna Mahmud Zakari Yau, mai shekaru 30 a duniya sun yi sa in sa da wani mai suna Basiru Mohammed da yake sana’ar Achaɓa wadda ya fito daga Yankin Zango Sa’idawa, a yayin sa in sar, shi Ya’u an yi zargin ya yi amfani da wuƙa ya caka wa Mohammed Dan acaba tare da yin awun gaba da babur ɗinsa kirar Bajaj launin Ja, mai lamba NNG813UM. Sai ko da aka yi sa’a Mohammed ya nemi ɗaukin mutane ta hanyar ihu, yadda maƙwabta suka kawo masa agaji tare da bin wanda ake zargin, hakan ya tilasta masa jefar da Babur ɗin, ya ranta cikin na Kare.
Bayanin ya ƙara da cewa Jami’an Yan sanda daga ofishin su dake Yelwa cikin hanzari sun isa wajen tare da ɗaukar wadda aka caka wa wuƙar zuwa Asibitin koyarwa na ATBUTH, inda likitoci suka bayyana ya rasu.
CSP Ahmad Wakil ya ƙara da cewa an ajiye gawar a Asibiti don kammala bincike da gwaje gwaje.
Kuma biyo bayan bincike an cafke wanda ake zargin ta hanyar bayanai da aka samu a cikin wayarsa da ya jefar da rigarsa mai dauke da wasu kayayyaki a cikin aljihun.
Yan sanda sun kira wasu lambobin mutane da yayi waya da su aka sanar da su cewa ya samu hatsari yana asibiti su zo. Da suka zo don kawo masa dauki aka cafke su aka je yadda yake aka kama shi.
Kuma a lokacin da ake tuhumarsa ya amsa laifinsa, inda ya alaƙanta yin kisan da cewa sharrin shaidan ne, DA kuma tsananin rashin kuɗin ƙara Mata ta uku, da hakan ya sa shi yaudarar Ɗan Achaɓan tare da caka masa wuƙa ya dauke mashin nasa don ya sayar ya samu kudin sadakin auren Mata ta uku da ya mata alkawarin aure amma abin da yake samu a sana’ar sa ta sayar da kayan marmari bata wadatar da shi yadda zai samu kudin cikawa matar alkawarin auren da ya yi mata ba.
Kakakin Rundunar yan’sanda CSP Mohammed Ahmed Wakil ya ce an samu shaida a wajen da suka hada da Babur Bajaj Boxer, wuƙa mai jini a jiki,Takalmi da wayar Salula ta wadda ake zargin.
Kwamishinan yan’sanda na Jihar Bauchi CP Sani Omolori Aliyu ya bada umarni a mai da binciken zuwa Sashen binciken manyan laifuka na Rundunar wato CID don ƙara bincike tare da gabatar da mai laifin gaban Kotu.

 

YAN SANDA A BAUCHI SUN CAFKE WANDA YA KWAKULE IDON KANWAR SA DA WANDA YA SA YA KAWO MASA IDON

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Bayan afkuwar wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a wani kauye da ke kusa da garin Wailo, a ƙaramar hukumar Ganjuwa ta jihar Bauchi, inda wani matashi mai suna Auwalu ya ƙwaƙwule idon ƙanwarsa yar shekara 7 mai suna Ruƙayya don neman biyan bukatarsa ta duniya, rundunar Yan sanda ta cika hannu da mutumin da wanda ya sa shi kawo masa idon.
Da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, mahaifin yarinyar, Malam Muhammad Adamu, ya bayyana cewa wanda ake zargin ɗan uwanta ne na jini amma ya ci amanar su ta hanyar yaudarar yarinyar yadda ya aikata Mata wannan ta’annati.
Ya ce Auwalu ya ja ƙanwarsa cikin daji bisa yaudara kafin ya aikata mata wannan mummunan aiki da ya bar ta da raunuka masu tsanani a idanuwanta biyu da ya kwakule.
Bayan tonuwar da asirinsa ya yi ne aka garzaya da Ruƙayya asibitin koyarwa na ATBUTH da ke Bauchi inda likitocin ido suka yi mata aiki don gyara wajen raunukan mazaunan idanuwan biyu.
Sai ko a cewar babban likitan asibitin ido na ATBUTH, Dr. Shahir Bello Umar, ƙwararren likitan ido yace ganinta ba zai sake dawo ba lamarin da ke nufin ta makance gaba ɗaya saboda ya lalata dukkan ido biyun.
Wani shaidar gani da ido da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatarwa wa manema labarai cewa tuni jami’an tsaro suka kama wanda ake zargi da aikata laifin, harma da wanda ake zargin shi ya saka shi ya nemo idon don aikata ayyukan tsafi.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi CSP Mohammed Ahmed Wakil ya tabbatar da abkuwar lamarin. Kuma kwamishinan Yan sanda na jihar Bauchi CP Omolarin Aliyu ya bayar da umarnin ci gaba da bincike don gurfanar da masu laifin a gaban kotu.

WANI : MAGIDANCI MAI MATA BIYU A BAUCHI YA KASHE DAN ACABA DON SAMUN KUDIN KARA AUREN MATA TA UKU
Share. Facebook Twitter LinkedIn Email Telegram WhatsApp

Related Posts

JIGAWA STATE IS A WRONG PLACE TO COMMIT CRIME AS AFFIRMED BY THE DECISIONS OF THE SUPREME COURT OF NIGERIA.

YAN FASHIN DAJI NA FAMA DA ANNOBAR AMAI DA GUDAWA, HAR TA YI AWON GABA DA WASU DAGA CIKIN SU ZUWA LAHIRA

KHADIJA ISAH THE 9 YEAR OLD VICTIM OF BRUTAL RAPE GOT JUSTICE .

GWAMNAN JIHAR JIGAWA MALAM UMAR NAMADI DAN MODI YA YI WA WASU MASU ZAMAN GIDAN GYARAN HALI AFUWA 12

GWAMNATIN JIHAR KANO TA DAUKI MATAKIN TSAURARA TSARO YAYIN SALLAR IDI DA ZA, A GABATAR NAN GABA KADAN DOMIN BIN DOKA DA ODA

TSOHON GWAMNAN JIHAR JIGAWA SULE LAMIDO DA YAYAN SA, ZASU CIGABA DA FUSKANTAR SHARI, A AKAN ZARGE – ZARGE DA HUKUMAR EFCC TAKE MUSU

Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Latest Posts

GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ZATA BULLO DA SABBIN DABARUN WARWARE MATSALOLIN MANOMA DA MAKIYAYA,TARE DA TANTANCE KAN IYAKOKI

April 14, 2026

AN SHAWARCI MALAMAI DAKE GUDANAR DA DA, AWAH DA SU DINGA KARANTAR DA WADANDA AKA MUSULUNTAR DOMIN SU SAN ADDININ MUSULUNCI, INJI BARR, YAHYA IBRAHIM ALIYU R

April 14, 2026

GWAMNAN JIHAR JIGAWA MALAM UMAR NAMADI DAN MODI YA CE, ILIMI BABBAN JARI DOMIN CIGABAN JIHAR JIGAWA,DAMA KASA BAKI DAYA

April 12, 2026
Advertisement
© 2026 MURYAR AREWA A YAU. Developed ny: ENGRMKS & CO.
  • Home
  • About Us
  • Disclaimer
  • Get In Touch
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.