Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bai wa Radio Nigeria Kaduna tabbacin ci gaba da samun goyon bayan Gwamnatin Jihar Jigawa, yana mai jaddada cewa hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin biyu na da matukar muhimmanci wajen isar da sahihan bayanai ga jama’a da kuma karfafa hulda da al’umma a matakin kasa da kasa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Mukaddashin Daraktan Shiyyar Radio Nigeria Kaduna, Malam Lawal Ali Garba, tare da tawagarsa a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a Gidan Gwamnati da ke Dutse.
Yayin da yake maraba da tawagar, Gwamna Namadi ya bayyana Radio Nigeria Kaduna a matsayin “hukuma mai matukar tasiri a fannin aikin jarida a Nijeriya,” yana mai cewa fadin yankin da kafar yada labaran ke kaiwa ya sanya ta zama daya daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen isar da sako ga jama’a, musamman a matakin karkara.
Gwamnan ya gode wa mahukuntan gidan rediyon bisa karrama gwamnatinsa kan nasarorin da ta samu tare da mika masa tambarin yabo, yana mai cewa hakan zai kara musu kwarin gwiwa wajen yi wa al’ummar Jigawa aiki tukuru.
Ya ce, “Muna matukar godiya da wannan karamci. Wannan karramawa za ta kara mana azama wajen yin ayyuka masu amfani ga jama’ar Jihar Jigawa.”
Gwamna Namadi ya jaddada cewa duk da karuwar tasirin kafafen sada zumunta, rediyo na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen yada manufofi da ayyukan gwamnati, musamman a Arewacin Nijeriya.
Ya kuma sake tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Radio Nigeria Kaduna domin amfanin al’umma baki daya.
Tun da farko, Mukaddashin Daraktan Shiyyar, Malam Lawal Ali Garba, ya ce ziyarar na da nufin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Hukumar Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN) da Gwamnatin Jihar Jigawa.
Ya kuma isar da godiyar Darakta Janar na FRCN, Dakta Mohammad Bulama, bisa goyon bayan da gwamnatin jihar ke bai wa hukumar.
Malam Garba ya yabawa Gwamna Namadi kan nasarorin da aka samu a fannoni daban-daban da suka hada da ilimi, lafiya, noma, gine-gine da walwalar ma’aikata.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta kashe sama da naira biliyan takwas wajen tallafin karatu a kasafin kudin shekarar 2025 karkashin shirin Danmodi Students Care Programme, wanda ya shafi kusan dalibai 35,000.
Haka kuma, ya yabawa aiwatar da mafi karancin albashi na naira 70,000 ga ma’aikatan jihar, daukar ma’aikatan lafiya, farfado da shirin kiwon lafiya kyauta ga yara da mata masu juna biyu, gyare-gyaren noma da kuma bunkasa ababen more rayuwa a fadin jihar.
Ya kuma jinjinawa zaman lafiya da tsaro da ake samu a Jihar Jigawa tare da rangadin hulda da jama’a na Gwamna mai taken “Gwamnati da Jama’a,” wanda ya samu karbuwa a kafafen yada labarai na Radio Nigeria.
An kammala ziyarar ne da mika tambarin yabo ga Gwamna Umar Namadi domin girmama gudunmawar da yake bayarwa wajen cigaban Jihar Jigawa.
Related Posts
Add A Comment
