Jihar Jigawa Ta Hada Gwiwa da Hukumar Karɓar Korafe-Korafe ta Ƙasa Domin Inganta Adalci a Zamani
Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana aniyarta ta haɗa gwiwa da Hukumar Karɓar Korafe-Korafe ta Ƙasa domin ƙarfafa shirye-shiryen tabbatar da adalci ga al’umma.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ne ya bayyana hakan yayin da yake karɓar baƙuncin Kwamishinan Hukumar Karɓar Korafe-Korafe, Honarabul Barde Usman, wanda ya kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa.
Alhaji Dagaceri ya jaddada cewa Gwamnatin Jihar Jigawa da hukumar suna aiki tare domin magance take haƙƙin ‘yan ƙasa. Ya kuma tabbatar wa hukumar cewa gwamnatin jihar za ta ba ta cikakken goyon baya da haɗin kai domin cimma manufofin da suka sanya a gaba.
Tun da farko, Honarabul Barde Usman ya bayyana cewa Hukumar Karɓar Korafe-Korafe wata hukuma ce mai zaman kanta wadda aikinta shi ne binciken rashin adalci a harkokin gudanarwa, cin zarafin iko, da kuma gazawar aiki daga hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. Ya ƙara da cewa manufar hukumar ita ce samar wa ‘yan ƙasa mafita cikin sauƙi da kuma ba tare da wani kuɗi ba.
Ya kuma bayyana manyan ayyukan hukumar da suka haɗa da duba matakan gudanarwa da ba su dace ba, sasanta rikice-rikice, da kuma inganta gaskiya da riƙon amana a aikin gwamnati. Kwamishinan ya roƙi Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar da ya ba su goyon baya da haɗin kai domin su samu damar cika waɗannan manufofi yadda ya kamata.
Related Posts
Add A Comment
