Gwamna Yusuf Ya Yaba wa Sarakuna, Malamai da Gwamnonin Arewa maso Yamma kan Nasarar Daurin Auren Ma’aurata
Ranar 08/08/2026
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana godiyarsa ga sarakunan gargajiya, malaman addinin Musulunci, gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma da sauran manyan baki, bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ganin an samu nasarar shirin daukar nauyin daurin auren ma’aurata da dama a lokaci guda da gwamnatin jihar ta shirya.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Asabar.
Gwamna Yusuf ya bayyana godiya ta musamman ga Shugaban Majalisar Sarakunan Kano da kuma Sarakunan Kano, Rano, Karaye da Gaya, bisa irin shawarwari na uba, addu’o’i da kuma muhimmiyar gudunmawar da suka bayar wajen gudanar da bikin.
Haka kuma, Gwamnan ya yaba wa malaman addinin Musulunci da suka yi tattaki daga sassa daban-daban na kasar domin halartar bikin, inda ya bayyana cewa addu’o’insu da shawarwarin da suka bayar sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar shirin.
Gwamna Yusuf ya kuma yabawa takwarorinsa na jihohin Arewa maso Yamma, ciki har da Gwamnan Jihar Katsina, Umar Dikko Radda; Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi; da Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, da kuma wakilansu, bisa girmama bikin da kuma halartar taron.
Haka zalika, Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga shugabanci da ma’aikatan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, karkashin jagorancin Kwamandan-Janar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, bisa jajircewarsu da sadaukarwarsu wajen inganta kyawawan dabi’u, zaman lafiya da walwalar al’umma.
Gwamna Yusuf ya kuma mika godiyarsa ga ’yan kasuwa, jami’an diflomasiyya, kungiyoyin farar hula, abokan huldar ci gaba da sauran baki da suka halarci bikin ko kuma suka aike da sakonnin fatan alheri.
Ya bayyana cewa irin wannan hadin kai da goyon baya daga bangarori daban-daban ya taimaka matuka wajen tabbatar da nasarar shirin da kuma inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano.
Related Posts
Add A Comment
