Hon. Abdussalam Abdulkarim AA Zaura ya miƙa wa jamʼiyyar APC takardar neman takarar Sanatan Kano ta tsakiya., a Inuwar jam, iyyar Apc.
Zaura ya miƙa takardar yammacin wannan ranar Lahadi ne 26 ga watan April 2026, AA Zaura tare da Dubban magoya baya suka yiwa ofishin jam, iyyar Apc na Jihar kano tsinke tare da jiga – jigan jam, iyyar da masu ruwa da tsaki da manyan Daraktocin Yada manufa da tallata hajar AA ZAURA, irin su Hon Dahiru Ahmed Mai huddadu, suna cikin Ayarin AA zaura da suka Je ofishin jam, iyyar Apc dake kan titin Audu Bako way Jihar kano.
A jawabinsa yayin miƙa takardar Zaura ya ce, sun zo gaban jamʼiyyar ne domin cika ƙaʼida kasancewarsu masu biyayya ga dukkan tsare-tsaren jamʼiyyar.
Ya kuma fatan yin nasara ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf da dukkan waɗanda za su yi takara a jamʼiyyar ta APC.
Zaura ya samu tarba daga shugaban jamʼiyyar APC na Kano Malam Umar Haruna Doguwa da sauran shugabanninta.
AA Zaura mutum ne da yayi shura wajen tallafi da jinkai da kyauta.
Shugaban jam, iyyar Apc na Jihar kano Alh Haruna Umar Doguwa, ya karbi takardun neman tsanyawa takar kan ya Yabawa AA Zaura bisa yadda ya Ke yiwa jam, iyyar Apc da yayan jam, iyyar hidima da kuma irin yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf yanuna gamsuwa da takarar ta AA ZAURA,
Shugaban jam, iyyar Apc yayi wa AA ZAURA fatan Alheri bisa wannan takarar ta neman Sanatan Kano ta tsakiya.
