GWAMNATIN JIGAWA TA MIƘA WURIN GYARAN FADAR SARKIN HADEJIA
Gwamnatin Jihar Jigawa ta miƙa wurin da za a gudanar da aikin sake gina tare da gyaran Fadar Sarkin Hadejia.
Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim ne ya jagoranci bikin miƙa wurin aikin. An wakilce shi ne da Daraktan Harkokin Masarautu, Alhaji Babandi Habu Sule, inda ya bayyana cewa aikin na da nufin kare muhimmancin tarihi na fadar, inganta amfani da ita, tare da ƙara mata kyan gani da tsaro.
Malam Bala Ibrahim ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na ci gaba da kyautata alaƙa da cibiyoyin gargajiya a faɗin jihar.
A yayin bikin, Sakataren ya bukaci kamfanin da aka bai wa aikin da ya tabbatar an kammala aikin cikin lokaci kamar yadda aka tsara.
An gudanar da bikin ne a fadar Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje, tare da halartar Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Masarautu, Alhaji Baffale Abbas, Shugaban Sashen Ayyuka na ofishin SSG, Bala Dauda, da Jami’in Saye da Kaya, Nura Mu’azu.
Bikin ya haɗa da rattaba hannu kan takardar miƙa aikin tsakanin kamfanin da kuma Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Masarautu, Alhaji Baffale Abbas, a madadin Gwamnatin Jihar Jigawa.
A nasa jawabin, Sarkin Hadejia kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, Alhaji (Dr.) Adamu Abubakar Maje, ya nuna farin cikinsa kan wannan shiri, tare da tabbatar da ci gaba da goyon baya da haɗin kai daga masarautun jihar.
An wakilce Sarkin ne da Galadiman Hadejia, Alhaji Usman Abdul’aziz, wanda ya yabawa Gwamna Malam Umar A. Namadi bisa samar da kyakkyawan yanayin aiki ga cibiyoyin gargajiya.
Shi ma dan kwangilar aikin, Alhaji Umar Kaila, Shugaban Kamfanin Kalahari Engineering Limited, ya yi alkawarin kammala aikin cikin inganci tare da bin wa’adin da aka ƙayyade a yarjejeniyar aikin.
