Majalisar Dokokin jihar Kano ta fito da wani ƙuduri da zai sanya gwamnati ta rika kula da irin kuɗaɗen makaranta da makarantu masu zaman kansu ke sanya wa iyaye a jihar.
Kudirin, mai taken ‘Kano State Private and Voluntary Institutions Board (Amendment) Bill, 2026’ zai taimaka wajen dakile ta’adar nan ta karin kuɗaɗe na ba gaira ba dalili da makarantu masu zaman kansu ke yi a jihar.
Da ya ke zantawa da manema labarai, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini ya ce kudirin, idan ya zama doka, zai sanya makarantu masu zaman kansu su rika tuntubar kwamitin iyayen yara, PTA, kafin su yi wani karin kudi.
