Gidan Radio premier ya rawaito cewar, ofishin Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso ya bayyana cewa shugaban karamar hukumar zai ci gaba da rike mukaminsa, duk da hukuncin da Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke kan rikicin kujerar a ranar 24 ga Maris, 2026.
A cikin sanarwar manema labarai da aka fitar, an ce kotu ta umarci a dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an kammala sauraron karar daukaka kara da ke gaban Kotun Daukaka Kara, mai lamba K/85A/2026, wacce ta samo asali daga kara mai lamba K/746/2024.
Sanarwar ta kara da cewa tuni an mika dukkan takardun karar zuwa Kotun Daukaka Kara, don haka babu wani sauyi a shugabancin karamar hukumar har sai an yanke hukunci na karshe.
Ofishin ya bukaci al’ummar Kumbotso da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka da oda, tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana yayin da ake jiran hukuncin kotu.
Haka kuma, sanarwar ta tunatar da jama’a irin abin da ya faru a shari’ar zaben gwamnan Kano na 2023, inda gwamnan ya ci gaba da rike mukaminsa har sai da Kotun Koli ta tabbatar da shi.
A karshe, an roki Gwamnan Jihar Kano da ya tabbatar da cewa an kiyaye halin da ake ciki domin tabbatar da zaman lafiya da mutunta doka, yayin da ake jiran hukuncin Kotun Daukaka Kara.
Hafiz A Haruna
Mai Taimakawa Shugaban Karamar Hukuma kan Harkokin Yada Labarai.
Sai dai har yanzu masu sharhi Akan AL, amuran siyasa, da SHARI, a na cigaba da fadin Al, barkacin bakin sa bisa wannan lamari Mai cike da sarkakiya.
