Cibiyar tallafawa mabukata ta AA Zaura Foundation ta rarrabawa jarirai masu bukatar nonon uwa Madara, dake kwance a Asibitin sheikh Ishaq Rabi’u dake titin gidan zoo.
Mai magana da yawun AA Zaura Malam Dahiru Mai Huddadu, shine ya wakilci AA ZAURA, a wajen rabon madarar.
Mai huddadu ya bayyana cewar sun bada wannan tallafinne, saboda Allah domin Inganta rayuwar jarirai da Kuma Tallafawa iyayen yaran da suke mabukata ne.
Manufar dai itace ta taimakawa AL, umma Kamar yadda, cibiyar take bayyana wa.

Da yake Karin bayani Daraktan A sashin kula da Yara dake Asibitin. Dr, Yunus yace an Ajiye Kwarya a gurbinta bisa yadda aka tuna da jarirai marasa lafiya wadanda sune Yara manyan gobe aka basu tallafin madaurar da ke maye gurbin Nonon uwa, wannan ba karamin abin Alheri bane.
Babbar Jami, ar dake kula da Yara jarirai, a cikin Asibitin malama Fatima Kabir, ta bayyana cewar ana samun Yara masu wannan ciwo na karancin nonon uwa. Kuma Ana bukatar masu ruwa da tsaki su kawo tallafin ga yaran da iyayensu basu da karfi..

Iyaye Mata dake jiyyar yayansu jarirai a Asibitin na sheikh Ishaq Rabi’u, sun yabbawa AA ZAURA FOUNDATION bisa wannan tallafin madarar da ya bayar fatan hakan zai dore.
Cibiyar AA Zaura Foundation dai ta shahara wajen taimakawa Al, umma, ta fuskokin da dama da suka hada da taimakawa marasa lafiya da taimakawa Dalibai da bada gudunmawa ga makarantun Alkur, ani maigirma.
