Sanata kawu sumaila wanda ya gana da matasa masu harkar sadarwa ta kafafen sadarwa na zamani dasu, tabbata sun tallata ayyukan shugaban Gwamnatin Nijeriya sanata Bola Ahmad Tunubu domin kaucewa yan zariruga na wannan zamani.
Sanata kawu yashawarci matasan da cewar yanzu ne makiya suke kokarin bata gwamnatin bola tinubu da wasu matsalolli da ta gada tun daga marigayi malam Umar musa ya’r adu,a.

Sumaila yace shugaban kasa Tunubu yafara cika alkawarin game da Ayyukan raya kasa ga yankin Arewacin nijeriya,domin inganta yakin domin cigba mai ma,ana Kuma Mai,dorewa.
“..wajibine a fito fili a tallata ayyukan shugaban kasa sanata Bola Ahmad Tunubu,domin kakkabe yan kama wuri zauna a siyasance.”
Daruruwan matasa ne daga yankin kano ta kudu suka halarci taron Wanda aka gudanar a dakin taro na Royal Dutse dake kusa da Titin Maiduguri,a judo yankin karamar hukumar Dawakin kudu.
Matasan Yan GWGWARMAYA sun amfana da kudade da Kuma takin zamani,
Tun a watannin baya sanata kawu sumaila ya bada kyautar injinan noman rani da haka rijiyoyi domin bunkasa noman rani a yankin kano ta kudu.
