Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa babban abin da yake nadama a rayuwarsa ta siyasa shi ne zaɓen Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a Legas yayin ƙaddamar da gidauniyar Charly Boy da kuma littafin tarihin rayuwarsa.
Ya ce da ace ya san halayen Atiku tun farko, da bai zaɓe shi a matsayin mataimakinsa ba.
Ya ƙara da cewa yana gode wa Allah saboda bai bari ayyuka da matakan Atiku su cutar da Najeriya ko su karkatar da gwamnatinsa daga abin da ya sa gaba ba.
Sai dai Obasanjo ya ce ba ya riƙe da wata ƙiyayya a zuciyarsa kan abin da ya faru tsakaninsu, yana mai cewa kowa ya yi abin da ya ga ya dace, yayin da Allah Ya ba shi damar cimma manufofin gwamnatinsa.
Obasanjo da Atiku sun jagoranci Najeriya tsakanin 1999 da 2007, amma daga baya rikicin siyasa ya ɓarke tsakaninsu, inda suka dade suna musayar zarge-zarge kan cin hanci, cin amanar siyasa da amfani da ofis ba daidai ba.
